✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ta’addanci: Gwamnan Zamfara da Ministan Tsaro na nuna wa juna yatsa

Gwamna Lawal Dare ya ce babu wani matsin lamba na cikin gida ko na waje da zai sa shi sasantawa da ’yan fashin daji

Gwamnatin Zamfara ta jaddada matsayinta na rashin yin sulhu da ’yan fashin daji, tana mai cewa babu wani matsin lamba da zai sa ta sasantawa da su.

Kakakin gwamnan jihar, Faruk Ahmad ne ya bayyana hakan a Gusau, a martaninsa ga kalaman tsohon gwamnan jihar kuma Karamin Ministan Tsaro na yanzu, Muhammad Bello Matawalle.

Ahmad ya bayyana cewa Gwamna Dauda Lawal na samun nasara a yaki da yake da ’yan fashin daji, kamar yadda fitaccen shugaban ’yan fashin daji, Bello Turji, ya bayyana.

A cikin wani bidiyo, Turji ya alakanta karuwar ayyukan ’yan fashin daji a Zamfara da sauran jihohin Arewa maso yammaci da tsare-tsaren Gwamnatin Matawalle.

A cewar Turji, daga ciki akai shirin yin afuwa, wanda ya bayar da tukuicin kudi da kariya ga ’yan fashin dajin da suka tuba suka mika makamansu.

Sai dai Matawalle ya bayyana ikirarin dan ta’addan a matsayin mara tushe balle makama, illa kokarin bata masa suna.

A wata sanarwa da sa hannun tsohon kwamishinan yada labarai gwamnatin Matawalle, Ibrahim Dosara, ya fitar, tsohon gwamnan ya zargi magajinsa, Gwamna Lawal da yin watsi da harkokin tsaron jihar.

Ya ce, “Abin takaici ne yadda ’yan bindiga suka Jihar Zamfara, babu wata karamar hukuma da ba a taba ba.

“Yanzu haka dai Gusau, babban birnin jihar, na fuskantar hare-haren ’yan bindiga a kullum.

“Ina shawararta Gwamnatin Dauda Lawal Dare ta maimakon makudan kudade da take batarwa wajen neman bata min suna, me zai hana ta yi amfani da su wajen kare rayuka da dukiyoyin Zamfarawa.”

Amma, a nasar martanin, Ahmad ya ce Gwamnatin Dauda Lawal za ta ci gaba da daukar matakan da suka dace don kawo karshen ta’addanci a Jihar Zamfara.

Ya kuma bayyana cewa a shirye gwamnan yake ya hada kai da duk wanda ya kuduri aniyar kwato Zamfara daga wannan bala’i.

Ya ce: “Mun gode wa Allah; an amsa addu’ar al’ummar Jihar Zamfara.

“Yanzu haka ’yan bindigar suna fito da muhimman bayanai kan wadanda suka dauki nauyinsu da kuma abokansu.

“Matakin da gwamnati mai ci ta dauka na magance matsalar rashin tsaro na haifar da sakamako mai kyau.

“Ina da yakinin cewa, sannu a hankali, Allah Madaukakin Sarki zai wanke da gwamnati mai ci.

“Ina kuma kara jaddada cewa, ba za mu sasanta da ’yan fashin daji ba, za mu ci gaba da yakar su, wadanda ke son mika wuya su yi, wadanda kuma ba su yi ba, za mu murkushe su su.”

Ya kuma musanta zargin da ke alakanta gwamnatin jihar Zamfara da shugabannin ’yan fashin dajin.

“Ta yaya za a ce gwamnatin da ta ki yin sulhu da ’yan fashin daji tana hada Hankali ma ba zai duaka ba.

“Masu alaka da ’yan fashin daji sun san kansu, mun gode Allah daya daga cikin ’yan fashin ya fara fasa kwai.