✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

’Yan bindiga sun kashe jarirai, sun bai wa karnuka namansu a Zamfara 

Ɗan majalisar ya ce a yanzu Zamfara ta zama tarkon mutuwa a wajen jama'ar gari.

Ɗan Majalisa mai wakiltar yankin Kaura Namoda da Birnin Magaji a jih6ar Zamfara, Hon. Aminu Sani Jaji, ya bayyana yadda ’yan bindiga suka bai wa karnuka wasu jairirai tagwaye da aka haifa a daji su ci.

Jaji, ya bayyana hakan ne a lokacin da yake zantawa da manema labarai a ranar Laraba.

Ya ce maharan sun sace wata mata mai ciki a wani ƙauye da ke Zamfara, kuma bayan ta haihu, ’yan bindigar suka jefa wa karnuka domin ci su.

Ya kuma ruwaito yadda wani yaro mai fama da cutar farfaɗiya ya mutu bayan da ya faɗi a dajin.

Ya ce ’yan bindigar sun nemi mahaifin yaron da ya miƙa musu shi, gudun ka da ya rasa sauran yaransa ya umarci yaron ya je wajensu.

Yaron ya yarda ya tafi, kuma nan take suka harbe shi har lahira.

Ɗan majalisar ya ce irin waɗannan abubuwa na nuna cewa gwamnati ta kasa kare mutane a Zamfara.

Ya buƙaci Gwamnatin Tarayya da ta ɗauki matakin gaggawa.

Ya bayyana yadda ya yi alƙawari kafin zaɓen 2023, inda ya faɗa wa jama’a cewa sabuwar gwamnati za ta bai wa tsaro muhimmanci, amma yanzu al’amura sun ƙara lalacewa.

“Mun cuci mutanenmu. Ba sa iya zuwa gonakinsu. Tattalin arziƙinsu ya rushe. Mutane da dama sun rasa matsuguninsu, kuma babu wani taimako daga gwamnati,” in ji shi.

Ya ce ya gana da wasu shugabannin tsaro har da Ministan Tsaro, amma babu wani canji da aka samu.

“Zamfara tana cikin aminci. Yanzu kuwa, tana daga cikin wuraren da rikici ya fi ƙamari. Kundin tsarin mulki ya ce gwamnati na da alhakin kare rayuka da dukiyoyi, amma hakan ba ya faruwa a yanzu.”

Da aka tambaye shi game da bai wa jama’a dama su kare kansu, sai ya ce doka ta fi komai.

“Mu ’yan majalisa ne, ba ma’aikatan tsaro ba. Ba za ce mutane su ɗauki makami ba. Amma gaskiya ne, mutane suna ganin yadda aka bar su,” in ji Jaji.