✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Yadda ’yan bindiga suka kashe dogarin Shugaban Kamfanin Jirgin Kasa

An harbe Sufeto Aminu har lahira a yayin da yake waya da iyalansa cewa ya kusa zuwa gida; Shugaban kamfanin jirgin kasan ya tsallake rijiya…

Manajan Daraktan Kamfanin Jiragen Kasa na Najeriya, Thimothy Zalanga, ya bayyana yadda ’yan bindiga suka bude wa ayarin motocinsa wuta, suka kashe dan sanda da ke tsaron lafiyarsa.

Mista Zalanga ya ce shi da sauran mutane da ke motarsa sun tsallake rijiya da baya ne bayan ’yan bindigar sun bude musu wuta dab da shigarsu garin Kaduna, bayan dawowarsu daga Abuja.

“An harbe Sufeto Aminu Muhammad da ke zaune a kujerar gaba har lahira, ni da direban da Sajan Allen Moses kuma mun tsallake rijiya da baya,” in ji shi.

Ya ci gaba da cewa, “Abin ya faru ne a lokacin da Sufeto Aminu yake tsaka da waya da iyalansa cewa ya kusa zuwa gida.”

A ziyarar ta’aziyyarsa ga Ofishin ’Yan Sanda na unguwar Donwn Quarters da ke Kaduna, Zalanga ya ce ’yan bindigar sun kai musu harin ne da misalin karfe 9 na dare ranar Lahadi, 18 ga watan Disamba, 2022.

Ya yi addu’ar samun rahama ga Sufeto Aminu Muhammad, tare da alkawarin cewa kamfanin zai ci gaba da tallafa wa iayalansa.

Kamfanin Jiragen Kasa na Najeriya wani rukuni ne karkashin Hukumar Jiragen Kasa ta Najeriya (NRC).

“Muna tuntubar iyalan marigayin, duk da cewa mun san babu wani abin da za mu iya yi da zai maye gurbinsa, amma za mu yi iya bakin kokarinmu wajen tallafa musu,” in ji shi.

Daga nan ya wa Sajan Moses da suka tsallake rijiya da baya tare tallafin kudi, ya kuma ba wa caji ofis din gudummawar babur, “domin saukaka muku aiki, saboda na samu bayanin yadda kuke fama a duk lokacin da kuka samu kiran gaggawa daga al’umma.

“Muna fata a farkon shekara mai zuwa mu ba da gudmmawar mota.”

A jawabinsa, DPO na Down Quarters, SP, Victor Allahmagani, ya yaba wa shugaban kamfanin jiragen kasan bisa ziyarar ta’aziyyar da kuma gudummawar, wadda ya ce za ta taimaka wajen saukaka musu ayyukansu.