✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Kauyakun Giwa: Yadda ’yan bindiga ke sheke ayarsu a watan Ramadan

A dare guda sun kai wa kauyuka akalla biyar hari suna kashewa da sace mutane tare da kona gidaje

’Yan bindiga na ci gaba da cin karensu babu babbaka, inda a cikin watan azumin suke kai hare-hare a yakin Giwa ta Yamma, suna aikata kisan gilla da sauran nau’ikan ta’asa.

Mahara sun yi ta afka wa yakin a lokuta daban-daban, a Unguwar Yamaimu da ke yankin Yakawada da ke Fatika a Karamar Hukumar Giwa suka yi yunkuri sace wani mutum mai suna Alhaji Haruna.

sai dai hakarsu ba ta cim ma ruwa ba sakamakon arangamar da suka yi da jami’an tsaro, wadda ta sa dole suka saki magidancin suka ranta a na kare.

A ranar ce kuma ’yan bindiga suka kuma kai wani hari a garin Marabar Guga, inda suka sace wani mai suna Alhaji Surajo da misalin karfe 12.30 na dare.

A cikin wannan dare dai, sun kuma kai hari ga wasu al’umomi wasu uku daban-daban duk a yankin karamar hukumar ta Giwa.

Kauyukan sun hada da Dan Kawo da Anguwar Gaga da kuma Dokan Ganga inda suka rika yin harbin kan mai uwa da wabi tare da banka wa gidaje wuta.

Daga nan kuma suka wuce zuwa yankin Tashar Sheri, duk a Karamar Hukumar Giwa ta Jihar Kaduna.

Wannan mataki na ’yan bindigar na alamta cewa sun mayar da yankin Karamar Hukumar Giwa fagen daga ke nan, inda suke cin karensu babu babbaka.

Tun kafin a shiga watan Ramada, akalla wata guda ke nan, kusan kullum da wuya a rasa labarin hari da kisan gilla a yankin na Giwa.

A ’yan satukan da suka wuce a baya, an yi ta fama da hare-haren ’yan bindiga a yankin, inda suke sace mutane, ciki har da masu sarauta, suna kuma aikata kisan gilla.

Wadannan hare-hare dai sun yi sanadin tserewar daruruwan mazauna yankin zuwa wasu wurare domin samun sa’ida daga ayyukan bata-garin.

A baya, Gwamnatin Jihar Kaduna, a wata ziyarar ta’aziyya da ta kai yankin, bayan wani kazamin hari, ta bayyana damuwarta kan yawaitar ayyukan ’yan ta’adda a yankin na Giwa.