✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Yadda ’yan bindiga ke samun miyagun kwayoyi a Sakkwato —Tambuwal

Galibi ’yan bindiga da masu satar mutane suna samun miyagun kwayoyi ne ta wannan hanya.

Gwamna Aminu Waziri Tambuwal, ya yi zargin cewa mata masu tallar Fura da Nono na fakewa da sana’ar wajen yi wa ’yan bindiga da sauran ’yan ta’adda a Jihar Sakkwato safarar miyagun kwayoyi.

Gwamnan ya yi furucin haka ne ranar Asabar yayin da fitaccen malamin addinin Islama, Sheikh Ahmed Gumi ya jagoranci shirin karbar tuban ’yan bindiga da aka yi wa lakabi GULBAR a birnin Shehu.

 “Wani takawarana, wani gwamna mai ci ya taba bani labarin wani abun da ya faru. Ya gaya mani cewa ta taba ziyartar wani kauye yana son sayen nono a wurin matan kauyen da suke fita cin kasuwar sayar da fura da nono.”

“Lokacin da ya kira su, sai daya daga cikinsu ta tsere. Ya tambayi dalili amma sai aka fada masa cewa ai ba tallar nono ta dauko ta fake ne da sana’ar amma miyagun kwayoyi ne a cikin kwaryarta.”

“Ya gaya mani cewa yawanci ’yan bindiga da masu satar mutane da sauran ’yan ta’adda suna samun miyagun kwayoyi ne ta wannan hanya.”

“A saboda wannan dalili, dole ne mu tashi tsaye domin shawo kan wannan matsalar ta sha da fataucin miyagun kwayoyi, don idan ba haka ba za mu karasa kashe macijin ne ba tare da sare kansa ba,” in ji Gwamnan.

A cewarsa, “ya kamata mu lura da irin rawar da miyagun kwayoyi ke takawa wajen rura wutar ta’addanci da sauran munanan halaye.”

Gwamnan ya jaddada cewa “addinin Musulunci addini ne na zaman lafiya kuma yada da’awa za ta taimaka wajen ceto ’yan uwanmu wadanda suke kan wannan mummunar sana’a ta satar mutane da ta’addancin Boko Haram da kashe-kashen mutane da asarar dukiya ba gaira ba dalili.”

Ya ce, “Da a ce akwai wadatacciyar tarbiyar addinin Musulunci da Tsoron Allah a zukatan mutane, da yawa daga cikin wannan munanan halaye ba za su taso ba.”

Ya yaba wa shirin karbar tuban ’yan bindiga da aka kaddamar a Jihar wanda a cewarsa zai taka rawar gani wajen cin moriyar baiwar da dama daga cikin ’yan ta’addan suke da ita sannan ya sha alwashin tallafa wa shirin.

%d bloggers like this: