✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Yadda ’yan bindiga ke cin karensu ba babbaka a Zariya

Ko a daren Asabar din da ta gabata, kimanin mutum 12 ne ’yan bindigar suka yi awon gaba da su.

…Sun kuma sace mutum 12

’Yan bindiga na ci gaba da cin karen su ba babbaka a Zariya da ke Jihar Kaduna inda suke kai hari wurare daban-daban a birnin suna sace mutane domin karbar kudin fansa.

Ko a daren Asabar din da ta gabata, kimanin mutum 12 ne ’yan bindigar suka yi awon gaba da su a sabuwar unguwar da ke tsakanin Kofar Gayan da Kofar Kona a birnin Zariya.

Majiyar Aminiya ta ce mutane takwas aka sace a gida daya,yayin da aka bi gidaje biyar aka dauko sauran.

Wata ganau, kuma diya ga daya daga cikin mutanen da aka sace, Hafsat Habib Kusfa, ta ce ’yan bindigar sun shiga gidan nasu ne da misalin karfe 12 na dare inda suka rinka bi daki-daki suna fito da mutane suna jera su a tsakar gida.

Ta bayyana cewa lokacin da suka shiga gidan na su, ’yan bindigar suna dauke ne da bindigogi da adduna kuma suna magana ne da harshen Fulatanci da Hausa lokacin da za su yi magana da mutanen da suka sacen.

Ta kara da cewa, bayan yin gardama a tsakanin su, sai suka ce mata ta koma gida domin ta kula da kananan yara da kishiyar mahaifiyar ta da ke jego.

Daya daga cikin wadanda aka sace iyalansu a unguwar Fammadina da ke Zariya

Ta ce, “Daga bisani sun tafi da mahaifina da mahaifiyata da kanne na da sauran ’yan uwa na. Gaba daya dai sun tafi da mutum takwas a gidan mu.

“Mun kuma ga wasu daga cikinsu sun fito da wasu mutane, galibin su maza daga gidajen makwabta inda suka tafi da su.

“’Yan bindiga bakwai ne suka shiga gidanmu wadanda na gansu da ido na, kuma akwai biyu daga cikinsu a waje da basu wuce shekara 30 ba, sai wasu da suke tsakanin shekara 15 zuwa 20,” a cewar Hafsat.

‘An sako iyayena daga bisani’

Har ila yau, Hafsat ta ce ranar Lahadi da safe ’yan bindigar sun sako mahaifinta da mahaifiyarta inda aka kai su asibiti domin duba lafiyar su kasancewar duk basa iya magana.

“Lokacin da suka dawo alamu sun nuna cewa sun sha duka a wurin ’yan bindigar,” kamar yadda ta bayyana.

Wasu rahotannin da ba a tabbatar ba sun ce ’yan bindigar sun kuma sace wani tsohon Manajan Banki a gidansa da ke Anguwar Graceland da ke Kwangila a Zariya a daren Juma’a da karfe misalin karfe tara na dare.

Kakakin Rundunar ’Yan Sanda na Jihar Kaduna, ASP Mohammed Jalige ya tabbatar da faruwar lamarin, sai dai yace basu tantance yawan mutanen da aka dauke ba.

‘Yadda na kubuta daga hannun ’yan bindiga’

Da yake bayanin yadda ya kubuta daga hannun masu garkuwa da mutanen, wani magidanci, Ibrahim Shehu ya ce bayan sun tasa keyarshi sai suka hada shi da mutum daya ya kula da shi a lokacin da suka shiga gidan makwabcinsa.

Malam Ibrahim Shehu kenan, wanda ya sha da kyar a hannun ‘yan bindiga

Ya ce ganin haka sai ya ga dama ta samu da zai iya kubucewa tun da ya fi shi sanin unguwar sai kuwa ya ranta da gudu inda suka bishi da sara amma bai tsaya ba duk da raunukan da suka yi masa a kai da fuskarsa.

Ya ce Allah ne ya taimakeshi ya buya a wani lungu har sai da aka fara kiran sallar Asuba kafin ya fito zuwa gida, daga nan kuma aka wuce da shi asibiti.

Kazalika, wata mata mai suna Hafsat Mustapha wacce aka tafi da mijinta kuma ta kasa magana saboda kuka da takaicin abinda ya faru inda ta ce kwana 47 da rasuwar mahaifin maigidanta ba su farfado daga juyayin ba kuma sai ga wannan ta faru.