’Yan Arewa mazauna Anambra sun kada kuri’arsu lami lafiya a zaben gwamnan jihar da aka gudanar ranar Asabar.
Binciken da Aminiya ta gudanar a garin Awka, babban birnin jihar da kuma garin Anaca, ya tabbatar da cewa ba a hantari ’yan Arewar ba, ballantana a gaya musu wata bakar magana a lokacin zaben.
An dauki tsauraran matakan tsaro ga duk wani wanda ke jin shi tsagera ne ko takadari da ke son tayar da fitina a lokacin zaben na Anambra, wanda da farko ake yi ta zullumi kansa, bayan kungiyar a-waren IPOB ta yi barazanar hana mutane fita, kafin daga baya ta sauya matsayi.
Muhammad Sunusi, mazaunin Awka, ya shaida wa Aminiya cewa, “Na fita na yi zabe, na kada kuri’ata da misalin karfe 11 na safe kuma duk inda aka ajiye akwatun zabe da ’yan Arewa suke kowannenmu ya fita ya fefa kuri’a ba tare [da wani ya] yi masa ko da kallon banza ko harara ba,” inji shi.
Ya ci gaba da cewa “An baza jami’an tsaro a ko’ina, babu wani wanda ya isa ya ce zai fito ya kawo cikas.”
Haka abin yake ma a garin Anaca, birnin kasuwanci mafi girma a jihar, inda aka gudamar da zaben lami-lafiya ba tare da an tashi hankalin wani dan Arewa ko dan asalin jihar ba, kamar yadda Alhaji Muhammad Sabo Wudil ya shaida wa wakilinmu.
“Akwatunan zabe da aka kawo mana tun daga ma kofar gidan Sarkin Nupawa da kuma sauran kusfa-kusfa da ’yan Arewa suke kowa ya kada kuri’arsa cikin kwanciyar hankali.
“Zancen nan da muke yi da kai na dade da dawowa daga jefa tawa kuri’ar kuma lafiya lau babu wata matsala; Duk ’yan Arewa mazauna Anaca muna zaune cimin koshin lafiya babu wani abu da ya same mu,” kamar yadda ya bayyana.
Kazalika ya ce, “An jibge jami’an tsaro fululu a ko’ina, babu yadda ma za a yi wani ya fito ya ce zai iya yin rashin kunya ko tayar da fitina.”