✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Yadda yajin aikin ASUU ya girgiza tattalin arzikin al’ummar Zariya

Yajin aikin bai tsaya iya dalibai da malamai ba don kuwa ya shafi ita kanta gwamnati.

Hasashe ya nuna cewa, al’ummar garin Zariya da ke Jihar Kaduna sun fi kowa jin radadin yajin aikin Kungiyar Malaman Jami’o’i (ASUU) ta fuskar tattalin arziki.

Masana tattalin arziki sun ce kasancewar garin Zariya shi ne kan gaba wajen tara cibiyoyin ilimi da dama, ya sanya harkokin kasuwanci da sufuri sun ja baya saboda yajin malaman jami’o’in.

Farfesa Bello Dogarawa, malami a Sashen Koyar da Lissafi kuma masanin tattalin arziki da ke Jami’ar Ahmadu Bello ta Zariya, na daya daga cikin wadanda suka bayyana hasashensu a kan wannan lamari.

A tattauwarsa da wakilinmu a Zariya, ya ce kasancewar garin Zariya ya zama wata cibiyar koyar da duk wani fannin na ilimi da ake bukata a kasar, don haka ya zama matattarar ’yan kasa gaba daya.

Malamin ya ce Jami’ar ita ce wadda ta hada ’yan kasa baki daya domin kusan duk Kananan Hukumomin Najeriya 774 da ake da su a jihohin kasar nan suna da wakili a Zariya.

Masanin ya kara da cewa, idan aka dauki cewa Jami’ar Ahmadu Bello tana da Dalibai dubu 40 kuma kowani dilibi zai kashe naira 100 da safe, 100 da rana, da yamma ma haka, idan ka lissafa kudin nawa zai kama?

Haka kuma ya ce ko yawan ma’aikata sun kai dubu takwas, baya ga ’yan kasuwa da suka dogara da daliban, sai kuma masu harkar sufuri, da sauran al’amuran yau da kullum.

“Saboda haka idan ka dubi masu cin abinci a wadannan cibiyoyin Allah kai dai Ya san iyakacinsu, don haka idan ka dubi barnar da yajin aikin ya haifar ba karama ba ce.

“Shi yajin aikin ya shafi ita kanta gwamnati saboda harkokin bincike da ake bukata daga Jami’o’in wadda ba karamar illa ce ga kasa ba sabanin yadda ake ganin cewar dalibai da masu gudanar da kasuwanci kadai ne yajin aikin ya shafa.

Aminiya ta gano cewa, wasu daga cikin ma’aikatan sun fara sayar da kadarorinsu domin biyan bukatun yau da kullum, lamarin da wasu daga cikinsu ke cewa yajin aikin bai amfana musu komai sai koma baya.