✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda ya kamata rayuwar Kirista ta kasance

Kun ji an fadi, ka yi kaunar makwabcinka, ka ki magabcinka: amma ni ina ce muku, Ku yi kaunar magabtanku, kuma wadanda su kan tsananta…

Kun ji an fadi, ka yi kaunar makwabcinka, ka ki magabcinka: amma ni ina ce muku, Ku yi kaunar magabtanku, kuma wadanda su kan tsananta muku, ku yi musu addu’a; domin ku zama ’ya’yan Ubanku Wanda ke cikin sama: gama Yakan sa rana tasa ta fito wa miyagu da nagargaru, Yakan aiko da ruwa bisa masu adalci da marasa adalci. Gama idan kuna kaunar wadanda ke kaunarku, wace lada ke gare ku? Ko masu karbar haraji ba haka suke yi ba? Idan kuwa kuna gaida ’yan uwanku kadai, ina kuka fi wadansu? Ko al’ummai ba haka suke yi ba? Ku fa za ku zama cikakku, kamar yadda Ubanku na sama cikakke ne.” (Matta:5: 43– 48). Kuma “Kada ku zama mabaratan komai ga kowa, sai dai na kaunar juna, gama wanda ya kaunaci makwabcinsa ya cika shari’a. gama wannan ba za ka yi zina ba. Ba za ka yi kisan kai ba. Ba za ka yi sata ba. Ba za ka yi kyashi ba, kuma idan da wata doka, an tarke ta cikin wannan magana, cewa, sai ka yi kaunar makwabcinka kamar ranka. kauna ba ta aika mugunta ga makwabcinta ba; kauna fa cikar shari’a ce.” (Romawa:13: 8–10).
Maganar Allah tana cewa; “Kun ji an fadi, ka yi kaunar makwabcinka, ka ki magabcinka.” Irin wannan rayuwa, ita ce ta fi sauki a cikin duniya; amma kafin mu ci gaba, ina so mu gane wane ne makwabci; haka nan nan kuma wane ne magabci; idan har mun gane ma’anar wadannan kalmomin sosai, za mu fahimci koyarwar Yesu ga almajiransa, wato wadanda suka rigaya suka ba da gaskiya gare shi.
Tambaya ta farko ita ce: Wane ne makwabcina? Akwai wani wanda ya yin irin wannan tambaya a cikin Littafi Mai tsarki, bari mu duba tare daga cikin Luka:10: 27– 37: “Ya amsa ya ce, sai ka kaunaci Ubangiji Allahnka da dukan zuciyarka da dukan ranka da dukan karfinka da dukan azancinka, da makwabcinka kuma kamar ranka. Ya ce masa, ka amsa daidai: ka aika wannan za ka yi rai. Amma shi, domin yana so ya baratar da kansa ya ce wa Yesu, WANE NE MAkWABCINA? Yesu ya amsa ya ce, Wani mutum yana tafiya daga Urushalima zuwa Jerico; ya gamu da mafasa, suka yi masa tsiraici, suka dudduke shi, suka tashi, suka bar shi tsakanin rai da mutuwa. Ya rarafa sai ga wani Malami yana bin wannan hanya: sa’anda ya gan shi, ya raba ta wancan gefe ya wuce. Haka nan kuma wani Lawi, sa’anda ya zo wurin, ya gan shi, shi kuma ya raba ta wancan gefe, ya wuce. Amma wani Ba-Samariye yana cikin tafiya, ya kawo wurin da yake: sa’anda ya gan shi, ya yi juyayi, ya zo wurinsa, ya daure raunukansa, yana zuba musu mai da ruwan anab; ya hawar da shi bisa dabbarsa, ya zo da shi wani mashidi, ya yi dawainiya da shi. Washegari kuma ya fita da sule biyu, ya ba Ubangijin mashidi, ya ce, ka yi dawainiya da shi; abin da za ka batar gaba da wannan, sa’anda na komo, na mayar maka. A cikin wadannan uku fa, wa ka aza ya zama makwabci ga wanda ya gamu da mafasa? Ya ce, wannan da ya nuna masa jinkai, Yesu ya ce masa, je ka, ka yi haka nan.”
Ba abu mai wuya ba ne mutum ya kaunaci abokinsa, ko kuwa wanda yake kusa da shi. Wannan kowa zai iya yi a sauwake. Damuwar takan zo ne a lokacin da aka ce ga wani yana gaba da kai, kuma ka sani; sai a ce da kai ka kaunaci irin wannan mutum – gaskiyar ita ce ba ta da sauki ko kadan. Mutanen duniya sukan ce, ka so mai sonka ka kuma ki mai kinka, idan har wani ya san cewa wannan mutumin, yana shirya maka makarkashiya; yana so ya yi maka rauni, abin da ya kamata ka yi bisa tunanin mutum, shi ne ka rabu da hanyar mutumin. Wani lokaci ko gaisuwa ma babu tsakaninku: kuma a cikin tunanin na ’yan Adam, babu laifi ko kadan cikin irin wannan hali. Amma ga mai ba da gaskiya ga Yesu Kiristi, koda yake mai yiwuwa muna da cikakken hujja mu yi kamar sauran mutane, ba za mu iya yin haka ba tare da saba wa koyawar Ubangijinmu Yesu Kiristi ba.
Masu bi a yau suna fuskantar tsanani sosai ta fannoni daban-daban; watakila kana zama da wani da ba ya so ya ganka da rai, mai yiwuwa har da iyalinka duka, ba abin mamaki ba ne kuma a yanzu; mun ga makwabtan da suka hada baki da wasu suka zo suka yi wa iyalan masu bin Yesu Kiristi yankan rago a gidansu. Wani lokaci ba kisa ba ne amma nuna bambanci a wurin aiki, mai yiwuwa, ka yi yi karatu ka kuma kware a filin karatunka, amma idan lokaci ya yi da ya kamata ka yi shugabancin wancan sashi, sai ka ga an dauko wani da kai ka koyar da shi, a ba shi wancan mukami; a dora shi bisanka kawai domin addini – kai Kirista ne; an so ka dauki umurni daga wurin wanda kai ka sani cewa dalibinka ne; ba abu ne mai sauki ba ko kadan.
Muna gani yau da kullum yana faruwa. A cikin irin wannan yanayi; mene ne ya kamata masu bin Yesu Kiristi su yi? Ubangijinmu Yesu Kiristi da kansa ya ba asirin tafiya da irin wadannan mutane. A cikin koyarwarsa na Littafin Matta: 5: 44, Yesu Kiristi ya ce “Amma ni ina ce muku, ku yi kaunar magabtanku, kuma wadanda sukan tsananta muku, ku yi musu addu’a.”