✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Yadda wutar lantarki ta kashe barawon wayar wuta a Gombe

Har yanzu dai ba a iya gane barawon ba.

Wani mutum da ake kyautata zaton barawo ne ya rasa ransa a lokacin da yake tsaka da kokarin satar wayar wutar lantarki a unguwar Labour Quarters da ke Tumfure a Karamar Hukumar Akko a Jihar Gombe.

Shugaban Sashin Sadarwa na Kamfanin Rarraba Wutar lantarki na Shiyyar Jos (JEDC) a Gombe, Dokta Adakole Elijah, ya tabbatar da faruwar hakan ranar Alhamis a Gombe.

Ya ce lamarin ya faru ne da misalin karfe 3:30 na safiyar ranar Alhamis inda wuta ta kashe wanda ake zargi da satar a yayin da yake tsaka da sace wayar wutar da ke jikin na’urar raba hasken wutar wato transformer da ke bai wa unguwar Tumfure wuta.

“Barawon ya yi kokarin lalata wayar ne da ke raba wutar a cikin Transfomer din” a cewarsu.

Ya kara da cewa an kai rahoton faruwar hakan ne a ofishin ’yan sanda na shiyya da ke Tumfure wato, inda ’yan sandan suka yi kokari suka sauko da gawarshi, duk da dai an gagara gane shi.

Ya roki mazauna wannan unguwa da su zama masu sa ido sannan su kai rahoton duk wani abu da ba su gane ba na masu barnata wayar wutar.

Ya kuma hori masu wannan dabi’a ta satar wayar wuta da su guji aikata wannan sana’ar saboda hatsarin da ke cikinta da kuma yadda suke jefa al’umma da kamfanin JEDC cikin duhu da asara.

Wani mazaunin wannan unguwa Zakari John, ya shaida wa wakilin mu cewa ba wannan ne karon farko da hakan ke faruwa ba a yankin, kuma hakan na jefa su zama cikin duhu a duk inda irin hakan ta faru.

John ya ce unguwarsu ta shiga cikin duhu na tsawon kwanaki bakwai a baya lokacin da taransufomarsu ta lalace.

“A lokacin da muka hada kudi muka gineta don ta tsira, amma sai ga shi barayin na zuwa dan sace wayar a cikinta.