Manhajar sadarwa ta sada zumunta ta WhatsApp ta sake samun matsala inda ta tsaya da aiki na tsawon mintuna a ranar Laraba.
Wannan dai ba shi ne karon farko da manhajar ta sada zumunta ta samu matsala ba.
A shekarar da ta gabata manhajar ta samu matsala a kasashe da dama ciki har da nahiyar Turai.
Lamarin da ya sanya miliyoyin mutane samun tsaikon tura sako ko karbar sako.
Kamfanin WhatsApp ya wallafa wani rubutu a shafinsa na Twitter, inda ya bayyana cewar yana aiki tukuru don daidaita komai game sa manhajar.
Sai dai bayan shafe tsawon kusan minti 20 zuwa sama manhajar ta dawo aiki.
A wannan karo ma bincike ya gano cewar daina aiki manhajar ya shafi kasashe da dama na duniya da ke amfani da kafar sada zumuntar.