✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Tinubu ya bai wa Abdullahi Abbas muƙami

Shugaban ƙasa Bola Ahmad Tinubu ya naɗa shugaban jam’iyyar APC na jihar Kano, Alhaji Abdullahi Abbas a matsayin wakili a majalisar daraktocin Hukumar Bunƙasa Cigaban…

Shugaban ƙasa Bola Ahmad Tinubu ya naɗa shugaban jam’iyyar APC na jihar Kano, Alhaji Abdullahi Abbas a matsayin wakili a majalisar daraktocin Hukumar Bunƙasa Cigaban Shiyyar Arewa maso Gabas.

A ranar Larabar nan ne Shugaban ƙasa ya aike da ƙunshin sunayen zuwa ga Majalisar Dattawa.

Sauran sunayen da shugaban ƙasar ya tura sun haɗa da Janar Paul Tarfa a matsayin shugaba, Gambo Maikomo, Tsav Aondona, Cif Mutiu Lawal-Areh, Samuel Ouigbo da Frank Owhor.

Rikici ya barke a mazabar Abba Gida-Gida da Abdullahi Abbas a Kano

Ya kamata Abudllahi Abbas ya gaji Ambasada Ungogo

Akwai kuma Mohammad Alkali a matsayin Manajan Darakta, Musa Yashi Daraktan Gudanarwa na sashen bada tallafi, Ahmed Yahaya Daraktan Gudanarwa na sashen ayyukan yau da kullum, da Dr Abubakar Iliya Daraktan mulki da harkokin kuɗi.

Sai kuma wakilai biyu daga Ma’aikatar kuɗi da tsare-tsare.