Kotu ta ba da umarnin tsare Shugaban Jam’iyyar APC na Jihar Kano, Abdullahi Abbas, da kuma gurfanar da shi a gaban kuliya kan zargin barazanar kisa.
Babbar Koutn tarayya da ke zama a Kano ce ta sa a tsare, a bincika da kuma gurfanar da Abdullahi Abbas, kan zargin barazanar kisa, tayar da zaune tsaye da kuma kalaman ysana, ga Mahmoud Lamido.
- Taskun da karancin sabbin takardun Naira ya jefa mazauna karkara
- Atiku zai bude makarantar haddar Al-Kur’ani mai dalibai 500 a Kano
Mahmoud Lamido ya shaida wa kotun ta bakin lauyansa cewa shugaban jam’iyyar ya kira shi a wata yana barazana ga rayuwar sa da cewa, “Sai na batar da kai.”
Akalin koun, Mai Shari’a S.A Amobeda, ya dage sauraron karar zuwa ranar 16 ga Fabairun da muke ciki domin ’yan sanda su aiwatar da umarnin.
Jam’iyyar NNPP ta bayyana umarnin kotun da cewa babbar nasara ce ga tafiyar dimokuradiyya a Jihar Kano.
Kakakin kwamitin yakin neman zaben NNPP na jihar, Sunusi Bature ya yi zargin irin kalaman Abdullahi Abbas na iya kawo yamutsi a jihar.
A cewarsa, karo na biyu ke nan kotu na umartar Kwamishinan ’yan sandan Jihar Kano ya tsare shugaban APC na jihar.
Kawo yanzu dai ba a ji uffan daga bangaren APC ko rundunar ’yan sandan jihar ba.