✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Yadda wata mata ‘ta haifi jaki’ a Zariya

Wasu na al'ajabi wasu na shakkun yiwuwar dan Adam ya haifi dabba

An shiga rudani a unguwar Tudun Wadan Zariya, bayan wata mai juna biyu ta yi ikirarin haifar wani nau’in halitta mai kama da jaki.

Al’amarin matar mai suna Murja Abdulsalam, ya sanya mutane tururuwar zuwa gidanta da ke Layin Lemu domin ba wa idanunsu abinci.

Matar mai shekara 45 ta bayyana wa Aminiya cewa kafin ta haihu abin da ke cikin nata, “Yana min yawo kuma ba na iya tafiya sosai,..Na je asibiti an ce ruwa ne.

“Asibitin Dokta Umar nake zuwa; Na yi hoto sau biyu, sai ya nuna ba komai sai ruwa,” inji Murja wadda aka fi sani da suna Ansalo Mai Taliya.

Yadda aka yi haihuwar

A zantawarta da wakilinmu, Ansalo ta shaida mishi cewa wata mata ce ta cire mata abin daga cikinta da addu’a.

A cewarta, ta haifi abin ne ta gefe, bayan kusan shekara biyu da juna biyu, wanda saboda nauyinsa ba ta iya tafiya da kyau, ko da an hoto ruwa ake gani.

“A cikina ta cire min da addu’a…Ta gefe [na haife shi]”, inji Ansalo Mai Taliya.

Ta ce a tsawon lokacin da take dauke da cikin ta yi ta fama da miyagun mafarki, kafin a hada ta da matar da ta yi mata addu’ar.

Wakilinmu ya so ganin matar da Murja ta ce ta yi mata addu’ar, amma ta ce ai matar daga Kano take kuma ta riga ta tafi.

Wakilinmu ya ga gawar jinjirin jakin a ajiye a cikin wata bakar leda a gefen mai jegon, mutane na ta shigowa gidan suna kallo.

Aminiya ta nemi zantawa da mijin Ansalo, amma aka shaida wa wakilinmu cewa mijin nata ya yi bulaguro.

Mun kuma nemi zantawa da wasu masu rike da sarautar gargajiya da suka ziyarci gidan domin ganin jaririn, amma abin ya ci tura.

Labarin abin da Murja take ikirarin an fitar daga cikinta ya kawo rabuwar kai a tsakanin mazauna, wasu na mamaki wasu kuma suke tantamar yadda dan Adam zai haifi dabba.

Akwai ayar tambaya

Da yake bayani kan wannan batu, Shugaban Majalisan Malamai na Kungiyar Izala Reshen Jihar Kaduna, Imam Aliyu Abdullahi Telex, ya ce shi sihiri gaskiya ne kuma hakan na iya yiwuwa.

Sheikh Talex, wanda shi ne Limamin Tudun Jukun, ya ce akwai ayar tambaya game hanyar da aka bi wajen fitar da dan jakin daga cikin matar.

Ya kuma yi bayani da cewa ba ya kamata ga Musulmi ya yi imani da cewa bokaye da masu sihiri na amfani da ikonsu wurin aiwatar da abubuwa.

Malamin ya bayyana cewa a bisa mahangar Musulunci kowane jinsi na halitta yana haihuwar jinsinsa ne.