Wata dalibar Jami’ar Gwamnatin Tarayya da ke garin Oye a jihar Ekiti ta gamu da ajalinta lokacin ta ziyarci saurayinta.
Dalibar mai suna Fadera Oloyede ta ziyarci saurayin ne mai suna Maliki Ayi, wanda ke karatu a Kwalejin Kimiyya da Fasaha ta Jihar Osun da ke garin Iree, tare da kawarta.
Mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan jihar Osun, Yemisi Opalola, wacce ta tabbatar da faruwar lamarin, ta ce an kai gawar dalibar dakin ajiyar gawa na Asibitin Koyarwa na Jami’ar Kimiyya da Fasaha ta Ladoke Akintola (Lautech) da ke Ogbomoso domin gudanar da bincike a kan musabbabin mutuwarta.
“Mun kame kawar marigayiyar wacce ta yi mata rakiya zuwa gidan saurayin, ta kuma bayyana mana cewa dukkansu sun ci shinkafa cikin dare kafin daga bisani su wayi gari da gawar kawar tata”, inji DSP Opalola.
Ta kara da cewa ‘yan sanda na ci gaba da bincike a kan lamarin.
Jami’an ‘yan sandan dai sun gano gawar marigayiyar ne a wani waje da aka jefar da ita a daura da gidan saurayin wanda tuni ya tsere ake kuma nemansa ruwa a jallo.
Ko a karshen makon jiya ma a jihar Imo, an gano gawar wata daliba da ta saurayinta, abokin karatun ta, wadanda suka mutu bayan da budurwar ta ziyarce shi.