✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda wata amarya ta watsa wa kishiyarta ruwan guba a Zariya

A ranar Alhamis da ta gabata ce aka zargi wata amarya mai suna Huwaila da watsa wa kishiyarta ruwan guba a Zariya da ke Jihar…

A ranar Alhamis da ta gabata ce aka zargi wata amarya mai suna Huwaila da watsa wa kishiyarta ruwan guba a Zariya da ke Jihar Kaduna.

Lamarin wanda ya auku a gidansu da ke Unguwar Gakiya a Zariya da misalin karfe 7 na safe ya tayar da hankalin mazauna unguwar musamman ma’aurata. Binciken Aminiya ya nuna cewa amaryar da ake zargi da watsa wa kishiyarta ruwan, mai suna A’isha mata ne ga wani mutum mai suna Abdullahi.  Kuma bayanai sun nuna shi mai gidan baya gidan a ranar da abin ya faru sai dai kiransa aka yi aka sanar da shi ta waya.

Wani kanen A’isha mai suna Abubakar ya tabbatar sa aukuwar lamarin, inda ya ce tuni an tafi da ita wani asibiti da ke birnin Kairo a Kasar Masar domin duba lafiyarta.

Ya shaida wa Aminiya cewa an watsa mata ruwan guban ne a gadon baya, wanda duk da rigar sanyi da ke jikinta sai da fatar ta daye. “Allah Ya sa lokacin da Huwaila ta shiga sashen A’isha akwai rigar sanyi a cikinta, domin ta kammala shirya yaronta ke nan za ta kai shi asibiti, sai kawai ta ji an watsa mata abu a jiki.

“Ta fada mana cewa da ta watsa mata sai ta ji wani sanyi a jikinata kafin daga bisani ta fara jin kamar ana yankan naman jikinta. Kuma a gaban danta aka yi, shi kuma sai yana cewa Maman Roda ce! Maman Roda ce!!” inji shi.

Game da ko wani asibiti aka kai yayar tasa sai ya ce, “Jiya Litinin aka tafi da ita asibiti a Kasar Masar domin ci gaba da duba lafiyarta, kasancewar abin ya yi muni, ruwa ke fita a bayanta,” inji shi.

Sai dai kuma Aminiya ta samu labarin cewa ’yan’uwan ita A’ishan sun shigar da kara kotun Majistare da ke Hunkuyi a Karamar Hukumar Kudan a Jihar Kaduna.

Kotun ta tsayar da ranar 30 ga watan Nuwamba don ci gaba da  sauraron karar da aka kai ita Huwaila a bisa zargin watsa wa kishiyarta A’isha  ruwan guba.

Mai Shari’a Baban Ja’eh ya bayar da belin Huwaila a bisa sharuddan mutum biyu da za su tsaya mata a kan kudi Naira dubu 200 kowannensu.

Masu karar sun yi zargin cewa, ruwan guba ta watsa wa A’isha, amma ba a tabbatar da hakan ba tukun. Wata majiya kuma da ta ce maigidan ne ya ce wa amaryar ta je ta gaida uwargidan, saboda kaciya da aka yi wa danta. Tana shiga sai ita uwargidan ta ce me ya kawo ta gidana, sai ta hau ta da zagi. To, dama akwai ruwan shayi a gabanta, sai ta dauko domin ta watsa wa amaryar, amma sai ya watsu a jikinta, inji majiyar.

Aminiya ba ta samu damar jin ta bakin mijin nasu ba, kasancewar wadanda aka zanta da su sun nuna ba su da lambar wayarsa sannan kuma ba mazauni ba ne. Sai dai kuma akwai bayanai da ke nuna cewa manya suna kokarin sasanta lamarin, don su ci gaba da zamantakewarsu ta aure.

Da take bayyana ra’ayinta a kan batun, Shugabar Mata ta kungiyar Muryar Talaka ta Kasa, Hajiya Gambo Mamman Gusau ta bayyana abin da ya faru da A’isha a matsayin zalunci ne kuma za su bi kadin batun har sai an yi adalci ga wanda aka zalunta.

“Ina kuma yin kira ga mata da su sassauta kishi domin yau idan kin zo kin auri mijin mace to, dole ke ce a kasa da ita. Tun da ita ta hakura kika shigo har kika haihu. Kin ga ke nan ai kun hada zuri’a. Daya na iya mutuwa ta bar daya, kuma daya dole ta ci gaba da lura da ’ya’yan da aka bari. Ni irin wannan abu duk inda ya taso nakan tsaya har sai inda karfina ya kare domin ganin an yi wa wanda aka cuta adalci,” inji ta.

Kakakin Hukumar ’Yan Sandan Jihar Kaduna, DSP Yakubu Sabo ya bukaci a ba shi lokaci domin ya binciki yadda labarin yake kafin ya iya cewa komai a yanzu.