✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda wani ya aurar da ’ya’yansa mata biyu ga malaminsa ‘lokaci guda’

An bata shi kamar yadda yake a shari’a. Koda yake shi ma mijin nasu mun samu sakon takardar sakinsu daga gare shi.

Ana zargin wani mahaifi mai suna Umar Abubakar bisa laifin aurar da ’ya’yansa mata biyu ga wani malaminsa mai suna Gausu Mustapha a Jihar Doso da ke Jamhuriyyar Nijar.

Tun farko wata mata ce wacce ta raini yaran bayan rasuwar mahaifiyarsu ta kai kara gaban Hukumar Hisbah ta Jihar Kano don a yi mata tsakani da mahaifin yaran wanda ta ce yana niyyar sake kwashe yaran don mayar da su hannun wancan malami kuma abokinsa.

Matar wacce ta nemi a boye sunanta ta shaida wa Aminiya cewa kasancewarta matar kakan yaran, lokacin da mahaifiyarsu ta rasu sai kakansu ya ba ta su don ta raine su.

“Bayan mahaifiyarsu ta rasu kakansu wanda ya haifi mahaifiyarsu ya dauko su ya ba ni su don in riƙe su. A lokacin babbar tana da shekara biyu ita kuma karamar tana wata 10.

“Bayan sun kai shekara goma a hannuna, sai babansu ya zo ya ce zai dauke su ya kai su wurin ’yan uwansa da ke Nijar domin ba su taba ganinsu ba.

“Haka muka dauke su muka ba shi. Tunda ya tafi da su bai sake dawowa da su ba, har aka yi shekara sai kakansu ya same shi ya ce tunda ya karɓe ’ya’yansa, to, ya nuna mana wurin da suke don mu je mu gan su ko kuma ya ba mu lambar wayar da za mu yi magana da su. Amma kememe ya ki, babu irin roƙon da maigida ba yi masa ba amma ya ki.

“Daga haka sai muka kai shi kara Hukumar Yaƙi da Fataucin Bil Adama (NAPTIP). Suka yi iya yin su don ya yi magana game da wurin da yaran suke amma ya ki. Hakan ya sa suka rufe shi. To bayan kwana biyu sai suka sake shi.

“A lokacin Hukumar NAPTIP ba ta faɗa mana dalilin da ya sa ta sake shi ba, amma a gefe mun samu labarin cewa wai yana da wasu manya a sama ne waɗanda suka yi ƙoƙarin fitar da shi.

“Haka dai muka hakura. A ƙarshe ma shi kakan yaran ya kamu da ciwon zuciya saboda baƙin cikin rashin yaran.

“Shi kuma mahaifinsu ba mu sake jin duriyarsa ba, mun je mun neme shi a wajen iyayensa su ma sun ce ba su san wurin da ya shiga ba,” in ji ta.

Matar ta kara da cewa ba ta sake jin duriyar yaran ba sai da aka yi shekara shida.

“Bayan shekara shida sai babbar yarinyar ta yi min magana ta Whatsapp ta ce wai ita da kanwarta suna Nijar a gidan wani malamin babansu mai suna Gausu.

“To a hirar da muka riƙa yi da su ne suka shaida min cewa wai malamin ma ya aure su duk su biyun.

“Haka suka riƙa rokona a kan in taimake su su fito daga hannun wannan mutum.

“Tun daga nan hankalina ya tashi na daura ɗamarar taimakonsu saboda ba su da kowa sai ni.

“Kasancewar sun shaida min cewa idan har babansu ya ji labarin, to, zai sa a kwashe su a kai su Benin, domin wai a lokacin da aka rufe baban nasu a NAPTIP, kwashe su aka yi aka kai su Benin aka voye su,” in ji ta.

Ta ce, “Sai na nemi taimakon ’yan uwan mahaifin yaran da suke Nijar. Da na je sai suka haɗa ni da wani alkali a Doso inda ya sa aka bincika aka gano cewa Gausun yana wani gari wai shi Bulbul a kusa da Gishime.

“Don haka sai ya nema mana jami’an tsaro muka tafi da su saboda an ce mutane ba sa zuwa wurin haka, kasancewar mutanen garin duk yaran Gausun ne. Ni a fahimtata ma ina zargin kamar bauta masa suke yi.

“Mun yi tafiyar kwana da yini ɗaya sannan muka isa. Da muka je suka ki yarda cewa yaran suna gidan har sai da aka yi rigima sannan da suka ga an fi karfinsu suka fito da yaran,” in ji ta.

Matar ta ce dama Gausun ya daɗe a tsare a hannun hukuma a Yamai, amma yana sanin duk abin da ake yi a gidan domin ana yin magana da shi ta waya ko a yi magana mai hoton bidiyo da shi.

“Don haka lokacin da muka je sai aka kira shi aka sanar da shi, sai ya ce a faɗa min ko na tafi da yaran sai ya sa an dawo masa da su.

“Ni kuma na ce na yarda a ba ni su, a ƙarshe na yi nasara na karɓo su muka taho da su. Jami’an tsaron nan suka yi mana rakiya har Birnin Kebbi na ɗauki kuɗi na biya su sannan suka koma. Sannan muka ƙaraso Kano,” in ji ta.

Ta ce, “Bayan mun dawo wata rana na tafi unguwa sai ga shi mahaifin yaran ya zo gidan wai zai ɗauki yaran don haka a yanzu na kai shi wurin hukuma don a yi min maganinsa.’’

Sai dai bayan kama shi da Hukumar Hisbah ta yi mahaifin yaran, Umar Abubakar ya ce, “Gausu Mustapha mutumina ne. Mun daɗe tare muna gudanar da ibadunmu tare.

“Kuma da ya nemi auren ’yata sai na ba shi, da suka rabu da dtayar sai na sake ba shi kanwarta. Abin da na sani komai za a yi a kan ’ya’yana yana sanar da ni domin ya ba ni hakkina na mahaifinsu.”

Yaran sun shaida wa Aminiya cewa ba su kaɗai ne matan Gausu da suke ’yan uwan juna ba. A cewarsu a cikin matansa ma har da wata uwa da ’ya’yanta. Sun ce, “Ba mu kaɗai ne ’yan uwan juna da muke matasa ba, akwai wasu da yawa.

“Haka kuma akwai wata mata ita da ’ya’yanta mata duk matan Gausu ne. Yana da matan aure da yawa.”

Yaran sun nemi hukuma ta taimaka musu kada mahaifinsu ya sake mayar da su hannun Gausu.

“Muna roƙon hukuma ta taimaka mana kada ta bari a sake mayar da mu gidan can,” in ji su.

Babban Kwamnadan Hukumar Hisbah ta Jihar Kano Shaikh Aminu Ibrahim Daurawa ya ce Hukumar Hisbah ta rushe auren yaran da wancan mutumin.

Haka kuma ya ce mahaifin yaran ya rubuta takarda da kansa cewa ba zai sake ɗaukar yaran ba ballantana ya mayar da su Nijar hannun malamin nasa.

Ya ce, “Mun bi abin da addinin Musulunci ya sanya, wato mun damka sha’anin tarbiyyar yaran a hannun dangin mahaifiyarsu.

“Shi kuma mahaifinsu mun sanya ya rubuta takarda bisa yarjejeniyar ba zai sake yunkurin ɗaukar yaran ba, ballantana ya yi batun mayar da su wurin malaminsa.

“Haka kuma wannan auren na yaran an bata shi kamar yadda yake a shari’a. Koda yake shi ma mijin nasu mun samu sakon takardar sakinsu daga gare shi.”