Mai gabatar da shirin nishadi na talabijin na Big Brother Naija da aka fi sani da BBNaija, Ebuka Obi-Uchendu ya ce gwarzon gasar shirin a bana zai fito ne ta hanyar samun kuri’u mafiya rinjaye.
Ebuka, a shafinsa na Twitter ya ce shirin wanda aka fara ranar 19 ga Yuli, 2020 da mutane 20 ya kusa zuwa karshe.
- Abinda ya sa shirin BBNaija ke daukar hankalin matasa
- Kannywood: Za a dawo haska fina-finai a sinima
Zuwa yanzu mutum biyar ne kacal suka rage a cikin shirin kuma duk wanda ya yi nasara a karshe zai samu kyautar Naira miliyan 85.
Shirin wanda a ne bana ake gabatar da shi a karo na biyar zai kawo karshe ranar Lahadi, 27 ga watan Satumba, 2020.
Wadanda suka samu zuwa zangon karshe na shirin sun hada da Laycon, Dorathy, Neo, Nengi da kuma Vee.
Kyautar kudaden da za a samu sun kunshi tsabar kudi Naira miliyan 30, gida mai dakunan kwana biyu, motar alfarma ta SUV kirar kamfanin Innoson, tafiya yawon shakatawa a birnin Dublin, wanda kamfanin Guinness ya dauki nauyi da kuma kayayyakin amfanin gida daga kamfanin Scanfrost.
Sauran kyaututtukan da sun hada da zuwa Dubai, taliyar da za a ci ta tsawon shekara guda, man goge baki na Colgate, lemon kwalba na sha na tsawon shekara guda, tafiya domin kallon wasan karshe na Gasar Zakarun Turai da kuma sabuwar wayar salula ta zamani.
A shekarar 2019 dai, Mercy Eke wacce ta lashe gasar shirin ta samu kyautar tsabar kudi Naira miliyan 30 da kuma wasu manyan kyaututtuka.