✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda uba da dansa suka lakada wa likita duka a asibiti

Lamarin ya faru ne bayan an sanar da mutumin mutuwar matarsa.

Wani uba da dansa sun lakada wa likitan Cibiyar Lafiya ta Tarayya da ke Idi-Aba a Jihar Abeokuta, duka bayan mutuwar matar mutumin mai shekara 53.

Shugaban Kungiyar Likitoci ta Najeriya a jihar, Dokta Kunle Ashimi ya tabbatar da faruwar lamarin, ya ce matar ta rasu ne sakamakon ciwon zuciya.

“Matar ta rasu da misalin karfe 2 na dare, bayan sanar da iyalinta sai mijinta da dansa suka hau likitan da ke kula da ita da duka.

“Akwai wata malamar jinya ma da suka ci zarafinta,” a cewarsa.

An ruwaito lamarin ya faru ne a ranar Talata, a sashen bayar da agajin gaggawa na asibitin lokacin da ta matar ta mutu.

Ashimi ya ce likitan mai suna Dokta Pelumi Somorin da wata malamar jinya da ba a bayyana sunanta ba sun sha dukan tsiya a hannun uba da dansa.

Ya ce uban da dansa sun mari likitan lokacin da ya sanar da su rasuwar matar.

A cewarsa, an kwantar da matar a asibitin ne sakamakon ciwon zuciya, wanda likitoci suka ce da kamar wuya ta tashi.

Shugaban ya ce tuni aka shaida wa ’yan sanda abin da ya faru, kuma dan marigayiyar bai daina cin zarafin mutane ba duk da zuwan ’yan sanda asibitin.

“’Yan sanda sun zo domin DPO ne da kansa ya jagoranci wata tawaga zuwa asibitin.

“Duk da ’yan sanda na wajen sai da dan marigayiyar ya ci gaba da cin zarafin malamar jinya an kasa shawo kansa.

“Daga baya ’yan sanda sun kwashe su zuwa caji ofis din Kemta kan tuhumar su bisa cin zarafin likita da kuma wata shaida (malamar jinya),” in ji shi.

Jin ta bakin kakakin ’yan sandan jihar, Abimbola Oyeyemi, ya ci tura zuwa lokacin hada wannan rahoto.