Wata Kotun Majistare dake zamanta a yankin Mapo na Ibadan babban birnin jihar Oyo a ranar Talata ta datse igiyar aure tsakanin wasu ma’aurata sakamakon tsoma bakin mahaifiyar mijinta cikin aurensu.
Matar ta zargi uwar mijin nata da mayar da ita tamkar baiwa mara ’yanci a gidanta.
- ‘Har yarzu matata na soyayya da tsohon mijinta’
- An yanke wa masu tsattsauran ra’ayi biyar hukuncin kisa a Bangladesh
- Buhari zai gina gidaje 10,000 masu saukin kudi a Kano
Da yake yanke hukuncin, Shugaban kotun, Mai Shari’a Ademola Odunade, ya bayyana cewa, kamata ya yi iyaye su zama masu bayar da shawarwari nagari a tsakanin ’yan’yansu ma’aurata ba jakadun haifar da matsaloli ba.
Odunade, ya yi Allah-wadai da gaza gani da shigar uwar mijin cikin sabgogin ma’auratan.
Daga karshe Alkalin ya datse igiyar auren ma’auratan ya kuma baya da umarnin matar ta ci gaba da rike dan da suka haifa, ya kuma ba mijin umarnin ya rika ba tsohuwar matar tasa naira N5,000 a kowanne wata don ta rika kula da su.
Tun da farko matar ta shaidawa kotun cewa, “Na bar gidan aure na saboda uwar mijina na son mayar da ni baiwa.
“Mijina ya gaza samar mana da abin da zamu ci da yaro na mai shekar hudu. Ya barni, ya yi tafiya zuwa Legas bayan ya rasa aikinsa a Ibadan.
“Babu wani tallafi da nake samu daga mahaifiyarsa, na dogara ne kadai da Iyaye na wurin abin da zamu ci, ina yi wa mahaifiyarsa aikatau don ta samu ta biya ni mu samu abinda zamu ci ni da yaro na amma bata biyana hakkina yadda ya kamata,” In ji ta.
Sai dai a nasa bangaren mijin nata, ha bayyana wa kotun cewa, shima yana bukatar a raba auren nasu saboda yana zargin matar tasa tana mu’amala da wani makwabcinsu, kuma yanzu haka tana dauke da cikin mutumin.
Mijin ya bukaci kotun da ta bashi dan da suka haifa ya rike a wurinsa saboda uwa ce ita mara kula kuma ba zata iya rike shi yadda ya kamata ba.