Mako guda kafin Babbar Sallah, al’ummar Musulmi na kokawa kan yadda ragunan Layya suka yi tashin gwauron zabo a Nejeriya.
Wasu da suka saba yin Layya sun ce bana da kyar za su iya saboda matsin tattalin arzikin da suke ciki, ko da yake wasu sun bayyana fata a bana ma za su samu su yi.
- Sabon Shirin Aminiya na WATA SABUWA
- Za a fara bikin kalankuwar ’yan fim a Kano
- Babbar Sallah: Kudin jirgi zuwa Arewacin Najeriya ya yi tashin gwauron zabo
Binciken Aminiya a kasuwannin dabbobi a sassan Najeriya ya gano farashin raguna ya karu da akalla kashi 70 cikin 100 ko ma ya ninku.
Wakilanmu sun gano matsakaicin rago da aka sayar N30,000 a Babbar Sallar 2019 da 2020 ya kai N50,000 a bana, babban rago da aka sayar N250,000 kuma ya kai N400,000.
Wani mai sayar da raguna a Kasuwar Zango da ke Tudun Wada Kaduna, Sunusi Usman, ya ce, “Idan har matsakaicin rago kake so a bana, to sai kana da N50,000 zuwa N60,000, babban rago kuma sai N100,000 zuwa N400,000”.
Sunusi ya an samu tsadar raguna shi ne sakamakon tsadar kudin mota, bayan tashin farashin man dizel da manyan motocin da ke dakon dabbobin ke amfani da shi.
Ranar Babbar Sallar 2022
Ban a Najeriya ranar Asabar 9 ga Yuli, 2022 ne za a yi Babbar Sallah, lokacin da ake yanka dabbar Layya domin neman yardar Allah.
Ibadar Layya koyi ne da Annabi Ibrahim (AS), wanda ya fara yin Layya a tarihi, bayan Allah Ya yi mishi jarabawa da ya yanka dansa tilo, Annabi Isma’il (AS).
Yin Layya na da dimbin lada, kuma ana yi ne da nau’ikan dabbobin ni’ima — tumaki da awaki da shanu da kuma karuma — maza ko mata.
An fi son yin Layya da rago saboda ya fi lada, sabanin Hadaya, wadda yi da rakumi ya fi lada.
Kasuwanin raguna
Aminiya ta samu masu sayar da dabbobi sun mamaye kasuwanni a Jihar Kaduna, sai dai kuma suna korafin rashin ciniki, mako guda kafin Babbar Sallah.
A karar da ke unguwar Kurmin Mashi a garin Kaduna, wani mai sayar da dabbobi, Ibrahim Aliyu, ya ce mutane na yawan zuwa kasuwar su duba raguna, amma kalilan ne ke iya saya.
“Mun san bana abubuwa sun yi wahala, amma duk da haka mutane na zargin mu da tsawwala kudin raguna.
“Ya kamata su fahimci ba laifinmu ba ne, yanzu kusan babu abin da kudinsa bai karu ba a Najeriya.
“Hatta masu turke dabbobin a gidaje za su gaya muku abincin dabbobi ya yi tsada, don haka hakuri kawai jama’a za su yi,” inji shi.
Wata Hajiya Halima Sani a garin na Kaduna ta ce ta zaga wuraren masu sayar da raguna da dama, kuma ta lura kudin rago mafi karanci shi ne N60,000 zuwa N75,000.
Shi kuma Usman Hamisu, wanda ya sayi ragunan N200,000, ya ce ya sayi daya N80,000 dayan kuma N120,000.
Malam Aliyu Suleiman mazaunin Zariya, ya ce da wuya bana ya samu yin Layya saboda yanayin tsadar rayuwa.
“Bana abubuwa sun yi tsada. Yanzu haka ta abin da iyalaina za su ci ranar Sallah nake; ko kaza na samu ya wadatar,” inji shi.
A Kasuwar Zango da ke Tudun Wada Kaduna, Malam Sunusi mai raguna ya ce farashin raguna ya fara ne daga N50,000 zuwa N400,000.
Borno:
Masu sayar da raguna a Maiduguri, Jihar Boro, suna kokawa kan rashin ciniki saboda tsadar dabbobin.
Bayan bude babbar hanyar Maiduguri zuwa Gamboru bayan samuwar zaman lafiya a sassan jihar, ’yan kasuwa sun je har kasashe irinsu Chadi da Kamaru sun sayo raguna domin sayarwa da Babbar Sallah.
Wakilinmu ya zaga kasuwanni da wasu sabbin wuraren sayar da raguna a garin, inda ya ga tarin raguna, amma masu sayarwa na cikin zullumi saboda rashin ciniki.
A babbar Kasuwan Shanu, Babagana Musa ya koka kan karancin ciniki saboda tsadar raguna.
Ya ce, “Rago mai kyau da aka sayar N100,000 yanzu N170,000 ne; Babba na N100,000 zuwa N150,000 a bara yanzu ya kai N250,000 zuwa N300,000 a bana. Yawanci tsadar abincin dabbobi ne ya jawo haka.”
Wani mai sayar da raguna a Kasuwar Raguna ta Bypass, Usman Lawan, shi ma ya koka kan rashin ciniki saboda tsadar dabbobin, wanda ya alakanta da hauhawan farashin abubuwa da kuma matsin tattalin arziki a jihar.
Bakari Mohammed, wanda ya je sayen rago ya ce ya kasa sayen matsakaicin rago.
Ya ce, “Na zo ne domin sayen ragon Layya dan matsakaici amma farashin ya fi karfin aljihuna.
“Irin ragon da na saya bara N50,000 yanzu N100,000 ne; amma zan jira in gani ko farashin zai ragu zuwa ranar jajibiri.”
Kano:
A Kano ma ba ta sauya zani ba, mutane na kokawa kan tsadar raguna, masu sayarwa ke bayyana cewa bana da kyar mutane ke iya sayen ragunan Sallah.
Wani magidanci mai ’ya’ya hudu, Tasi’u Musa, ya ce bana ba zai iya sayen ragon Layya, domin shi ta yadda zai ciyar da iyalansa yake kokari, ba ta ragon Layya ba.
Ya bayyana cewa ya shiga wani ginsami a unguwarsu domin sayen sa ko rakumi da za su raba naman su yi miyar Sallah, amma ya gagara.
Amma Shu’aibu Gambo, wanda ya sayi raguna biyu a Kasuwar ’Yan Awaki da ke Unguwa Uku, ya ce shekara guda ya shafe yana tara kudin.
Kakakin Kasuwar Dabbobi ta ’Yan Awaki, Umar Ado Kwari, ya ce suna da duk irin dabbar da mutum ke bukata a kasuwar.
“Duk da tsadar mutane na sayen raguna saboda akwai masu saukin kudi daidai da aljihun kowa,” in ji shi.
Abuja:
A Abuja, wakilinmu ya lura akwai karancin hadahadar dabbobi kamar yadda aka saba a kasuwanni irin su Dei Dei da Madalla da sauransu.
Ya’u Ahmed mai sayar da ragunu ya ce dabbobin sun yi karanci kuma babu ciniki kamar bara da dabbobi ne ko’ina a kasuwanni, babu masaka tsinke.
Dan kasuwar ya danganta matsalar da yanayin tsaro a yankin Aewa maso Yamma, inda ’yan bindiga suka tilasta wa makiyaya tserewa daga garuruwansu.
Wani abin kuma shi ne tsadar man dizel da ya ninku a kan bara, yana mai cewa abin ya kai ga karyewar jarin wasu ’yan kasuwa, wasu kuma ke kokarin yadda harkokinsu za su dore.
Wani mai sayen rago, Kamaruddeen Adelaja, ya ce ya kadu da yadda kudin raguna ya yi tashin gwauron zabo.
Ya ce “Na zo da niyyar sayen rago, amma yanayin kudin da na ji, dole na nemi wanda girmansa bai kai yadda nake so ba.”
Wata Kirista da muka hadu da ita a kasuwar wucin-gadi da ke Kubwa, Iwobi Ifeanyi, ta ce ta so sayen raguna 10 ta raba wa abokan arzikinta Musulmi su yi Layya kamar yadda ta saba a duk shekara, amma, “Na girgiza da yadda raukuna suka yi tsada, duk da kankantarsu. Na shafe awa uku ina yawo a kasuwar nan, amma na kasa yanke shawara,” inji ta.
Yankin Kudu:
A jihoin Legas da Edo da Imo da sauyan yankin Kudncin Najeriya, Musulmi na kokawa kan tsananin tsadar raguna.
A Kasuwar Shanu ta Eayen da ke Jihar Edo wakilinmu matsakaicin rago ya kai N80,000 zuwa N200,000 babba kuma N250,000 zuwa N400,000.
A Kasuwar Shanu ta Obinze kuma matsakaicin rago ya kai N180,000 wanda ya dara shi kuma N250,000 zuwa N300,000.
A Legas ma haka bin yake inda masu sayar da dabbobi ke kukan rashin ciniki duk da wahalar da suka yi na jigilar dabbobin daga yankin Arewa zuwa can.
Shugaban Kasuwar Shanu ta Eayen, Malam Aliko Haruna, ya ce tun da ya kawo dabbobi Benin bai sayar da ko guda daya ba.
“Kawo yanzu dai babu ciniki; Masu saye ba sa zuwa. Amma ina kyautata zaton kwana kadan kafin Sallah za su so su saya, saboda yawancin mutane ba su da wurin ajiye dabbobi, saboda haka suke bari sai kwana biyu ko daya kafin Sallah su saya.
“Muna da raguna har na N600,000, akwai na N400,000 da na N250,000 da kuma ragon N200,000.
“Amma matsakaicin rago yakan kai N80,000 zuwa sama, ragaon N50,000 dan kankani ne,” inji shi.
Ya kuma danganta matsalar da tsadar rayuwa da ake fama da ita a Najeriya a yanzu.
Wani wanda wakilinmu ya samu ya je sayen rago, Abdulaziz Isah, ya ce ya je da N70,000 domin sayen rago amma ya babu rago daidai kudinsa.
“Na karade kasuwar amma kudina ba za su iya sayen rago ba; Dole sai na koma gida na kara neman kudi,” inij shi.
Wani mai sayar da raguna a Oke Afa da ke Isolo a Jihar Legas, Abiola Hafeez, ya ce rashin tsaro ya hana shi zuwa Arewa sayo raguna; Saki ya je a Jihar Oyo ya sayo.
Ya ce wasu abokan sana’arsa da suka je Jihar Zamfara sayen raguna da kyar suka sha a lokacin da ’yan bindiga sun kai hari garin da suka je.
“Sai jarimi ke iya tafiya Arewa sayo dabbobi, amma ba kowa ba,” inji shi.
Kazeem Temitope, wanda ya ce duk shekara sai ya yi Layya, ya ce bana ma zai yi da yardar Allah, komai tsadar raguna.
Ya ce, “Sallah ana mata shiri ne kaifin ta zo. Na san mutanen da duk shekara sukan sayi rago biyu zuwa uku, amma sun ce bana daya za su yanka saboda tsadar dabbobin.
“Wani wanda ya saba yanka shanu kuma bana ya rage adadin da zai yanka; Mun san sun yi tsada, amma a haka za mu daure mu saya.”
Luqman Obanikoro ya ce saboda tsadar da raguna suka yi, bana dan karami zai nema ya yanka, maimakon ya zana bai yi Layya ba.
Daga Sagir Kano Saleh da Adam Umar (Abuja), Mohammed Ibrahim Yaba (Kaduna), Hassan Ibrahim (Maiduguri), Salim Umar Ibrahim (Kano), Usman A. Bello (Benin); Risikat Ramoni (Legas) & Jude Aguguo Owuamanam (Owerri).