✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda tsadar magunguna ke jefa marasa lafiya cikin kunci

Marasa lafiya a Najeriya na kokawa saboda tashin gwauron zabon farashin magunguna musamman ma na ciwon suga da na asma da na hawan jini

Bincike ya nuna masu dauke da kanana da sauran cututtuka gama-gari na fuskantar kalubale na tashin gwauron zabo da tsadar da magunguna na musamman ciwon suga da na asma da na hawan jini ta yadda suke matukar shan wahala kafin su iya siyansu.

Baya ga haka, wasu nau’ukan magungunan akan neme su a rasa a shagunan sayar da magunguna da asibitoci ta yadda sai mara lafiyar ya yi tafiya zuwa wani wuri mai nisa kuma a farashi mai tsada sabanin yadda ake sayar da shi a baya.

Aminiya ta ruwaito yadda lamarin ke neman ya gagari kundila musamman ga marasa lafiyar da cutar ta tsananta musu kamar masu dauke da cutar kansa da na zuciya da na huhu da kuma ciwon hanta ta yadda wasu suka koma neman maganin jifa-jifa ba a kai a kai yadda ya kamata a likitance ba.

An bayyana Nijeriya a matsayin kasar da tafi hadahadar magunguna da fiye da kashi 70 na magungunan da ake shigo da su daga kasashen Indiya da China da sauran kasashe.

Masana sun ce, fiye da kashi 70 na kudaden daukar nauyin sayen magunguna ga ’yan Nijeriya suna yin sa ne ta hanyar kananan kudaden shigar da suke samu da bai taka kara ya karya ba, ta yadda hakan ya zamo wani aikin gabas musamman ga talakawa saboda tashin farashin magunguna.

Dalilan hauhawar farashin magungunan

Shugaban Kungiyar Masu Hada Magunguna ta Kasa (PSN), Farfesa Cyril Usifo ya dora laifini tashin farashin magungunan ga sinadaran hada magungunan masu karfi (APIs).

“Abin a fili yake. Abubuwan da muke amfani da su wajen hada magungunan ba a nan (kasar) ake samar da su ba. Ya danganta da nawa muka kashe domin samo su zuwa nan.

“Bayan haka kuma, babu wutar lantarkin da zai iya harhada su. Ana amfani da injin janareto ne a nan kuma ka san farashin man dizel.

“A matsayinka na dan kasuwa idan har ka kashe makudan kudade irin wannan za ka siyar da shi ne da sauki?

“Idan ka kashe Kwabo daya ba za ka sayar da Kwabo daya da sisi ba ne don ka samu damar biyan ma’aikata ba?

“Ka ga amsar a fili take ke nan. Hanyoyi babu kyau, ka tafi misali zuwa Agbara za ka ga yadda wasu kan hada magungunan, amma daga lokacin da za a kwashe zuwa garuruwa za ka ga yadda motoci ke lalacewa saboda munin hanyoyin da suka lalace.

“Abin da nake cewa shi ne duk abubuwan da ke faruwa ba kawai ya tsaya ga fannin harkokin magunguna ba ne kawai. Gaskiya abin babu dadi domin a karshe za ka ga abubuwan da ke faruwa shi ne yayinda wasu masu sayar da magunguna ke sayen magani a misali Naira 2 to ba za su fada mana ainihin farashin ba (daga can). Da zarar an gama sayarwa an koma don sarowa sai ka ga ya koma Naira 5.

“Ba su ma iya mayar da uwar kudinsu ba ballantana riba amma kuma sai ka ga an fara kokawa da an ne sayen magani wurinsu. Kamfanonin dake yin magungunan nan su ke kara farashi cikin wata uku kawai. Wani ya fada min cewa sun karawa magunguna kudi fiye da sau uku,” inji shi.”

Shi ma Shugaban PSN na Jihar Borno, Umaru Abdulkareem ya ce, wani dalilin da ke haifar da tashin farashin magungunan ficewar kamfanoni na kasashen duniya irin su  GlaxoSmithKline (GSK) daga kasar.

Ya ce, a sakamakon haka ne farashin magungunan da suke samarwa irin su salbutamol da Ventolinda ake shakawa da wanda ake yi wa masu ciwon asma, ya yi tashin gwauron zabo.

Ya ce, maganin asma da ake sayarwa a da a kan farashi Naira 4,000 yanzu ya koma Naira 12,000.

Ya ce, yayin da kwayar magani Augmentin da ake sayarwa kan Naira 6,000 ya tashi zuwa 24,000, haka su ma magunguman ciwon zazzabi.

Yawancin kamfanonin harhada magunguna na kasashen waje da ke cikin Najeriya sun fice daga kasar a cikin ’yan watannin nan saboda damalmalewar harkokin kasuwanci.

Rugujewar harajin kudin mai da karancin Dala don shigo da kayayyaki daga waje sun taimaka wajen yi wa kamfanonin kasashen waje illa a kasar nan.

A watan Yunin da ya gabata an gargadi masu kamfanin harhada magunguna a Nijeriya yadda harkar musayen kudi zai haifar da karancin samar da magungunan da su ke yi saboda na za su iya cimma dukkanin nauye-nauyen da kasuwancin da dalar Amurka ta mamaye.

Tun a watan Agusta Kamfanin hada magunguna na kasar Birtaniya da ke Najeriya wato GSK, ya bayyana shirye-shiryen hada komatsansa don barin kasar.

Kamfanin GSK, wanda ya yi fice a Najeriya, musamman wurin sarrafa magunguna irin su, Panadol da Gishirin Andrew da Sensodyne, sun bar kasar bayan shafe shekaru 51 inda suka ce za su koma wani tsari na rarraba magungunan nasu a cikin kasar.

Yayin gudanar da babban taronsu karo na 52 a 2022, shugaban Kwamitin Daraktocin kungiyar, Edmund Onuzo ya ce kamfanin, wanda shi ne na biyu mafi girma wajen hada magunguna a Nijeriya ya koma tangal-tangal wajen rarraba magungunansu da allurai saboda karancin dalilin da za su shigo da sinadaran hade-haden.

“Kalubalen da ke gaba ma suna da yawa sosai. Wasu daga cikinku sun karanta rahotanni daga kafafen yada labarai game da halin da magungunan kamfanin GSK ke fuskanta a kasuwanni saboda matsin tattalin arziki.

“Dole mu bayyana ci gaba da fuskantar hakan tare da ci gaban karanci ko rashin samun wadatuwar harkar musayar kudade a kasuwancin da kudaden waje suka mamaye su,” inji shi

A watan Nuwamba ne kamfanin magunguna na Sanofi, mallakar kasar Faransa ya bi sahun takwaransa na GSK, inda ta bayyana shirinsa na dakatar da gudanar da harkokinsa a Najeriya.

Sun bayyana cewa, tuni har sun nada masu shiga tsakani da za su rika turo wa magungunansu don rabawa a kasuwanni zuwa nan da watan Fabrairun badi (2024).

A cikin wani ci gaba da aka samu, jaridar Aminiya ta bayyana yadda kamfanin 8KLOHYHU ya bayyana samar da canje-canje na yadda yake gudanar da harkokinsa don saukakawa wajen samar da magungunansa.

A cikin takardar kasafinta, kamfanin ta bayayana yin asarar wuri na gugar wuri har Naira biliyan 1.09 a wata tara na farkon shekarar 2023.

Yayin da rancen da suka yi ya karu daga Naira miliyan 328.89 zuwa Naira biliyan 1.03 a shekarar 2023 wanda yawanci tsarin Babban Bankin Nijeriya ya haifar musu da ita.

Kamfanin sun yi wasu asarar na dabam na sauye-sauye na kimanin Naira biliyan 3.27. Kamfanin Evans Medicals kuwa dama tun shekarar 2017 suka daina gudanar da komai a Nijeriya bayan umarnin kotu kan umurtar First Bank da ta amshe kadarorinsu da kuma na tsohuwar bankin Sky saboda mummunan bashin da ya lakume su.

Yadda yanayin yake a fadin jihoji

Mista Okeowo, wani ma’aikacin banki a Ibadan wanda ke karbar albashi kasa da dubu 70 wanda kuma mahaifiyarsa mai kimanin shekara 75 ke fama da ciwon hawan jini da yake dawainiya da ita na tsawon shekara 20 ya koka da yadda hauhawar farashin magunguna ke ta karuwa.

Ya ce, “A bara nakan kashe tsakanin Naira dubu 10 zuwa dubu 12 a kowane wata wajen saya wa mahaifiyata magunguna, amma a yanzu nakan kashe fiye da Naira dubu 20 kan wadannan magungunan kuma hakan yana fin karfin samuna, sai dai ba ni da wani zabi don ina neman albarkarta ne ta hanyar dawainiya da ita.

“Tsohuwa ce kuma ba ta da wani da ya wuce ni.”

Wani mai sayar da magunguna a kantin Jochem Pharm, mai suna Bashorun Ibadan, ya bayyana hauhawar farashin magungunan a matsayin wani abin tayar da hankali hatta ga masu sana’ar.

Ya ce wasu majinyatan sun gwammace siyan wasu nau’ukan magungunan sabanin wanda aka rubuta musu saboda neman sauki.

Da aka tambaye shi ko hakan ya rage adadin magungunan da ake sayarwa sai ya ce ko kadan.

“Mun dai fahimci kawai mutane kan bi magunguna masu saukin kudi ne kawai.

“Dole dai a sayi magani. Misali muna da kwayoyin Panadol daga kan Naira 500 zuwa na 200 da na 150 da kuma na Naira 100 kowane sacet daya, abin da muka lura da shi shi ne mutane kan bi mai arha ne,” in ji shi.

Wata malama a Jami’ar Ibadan mai suna Dokta Adegboye, wacce take fama da ciwon asma ta ce magunguna wani bangare ne mafi muhimmanci a rayuwarta.

“Ba zan iya kauce wa sayen magungunana ba domin sun fiye min abinci. Duk irin kukan da zan yi da tashin gwauron zabon farashin magungunan hakan ba zai hana ni saya ba, ina mamakin masu dauke da irin wannan lalurar da ba sai shan magunguna.

“Ya kamata gwamnati ta yi wani abu a kai don magani ba kayan kyalekyale ba ne,” inji ta.

Ita kuwa Mis Rebecca Gbenga wacce ta tattauna da wakilinmu a Legas ta koka ne kan ninka kudin da maganin da take saya ya yi.

Ta ce maganin ciwon idon da take digawa da ta saba saya kan Naira 1,200 yanzu ya koma Naira 1,800, inda ta ce hakan ya faru ne a kasa da mako guda kuma babu tabbacin sake saukowarsa.

“Ka je kowane shagon sayar da magunguna ka tambayi nawa ake sayar da Cusimolol maganin ciwon ido ka ji nawa ake sayar da shi yau kuma nawa yake makonni biyu da suka wuce.

“Ban san yaya zai kasance nan gaba ba.”

Wata mai sayar da magunguna mai suna Misis Nelly ta ce a kullum sai masu harhada magunguna sun kara musu kudin magani.

“Idan mun saya Gestid a yau misali a kan Naira 1,100, to washegari zai koma zuwa Naira 1,500, wannan ta bangaren masu rarrabawa ne.

“Yawancin ’yan Nijeriya ba sa jin dadin wannan yanayin babu yadda za su yi ne kawai.”

Ni na koma amfani da magungunan gargajiya ne kawai – Mai ciwon suga

Patrick Odiase wani mai dauke da ciwon suga a Jihar Edo ya ce yana cin bakar wahala wajen sayen magungunan sa a dalilin tashin farashin magunguna, abin da ya sa yawancin masu ciwon suka koma maganin gargajiya.

“Ina xauke da ciwon suga tsawon shekara 12 amma yanzu abubuwa sun rikice saboda tsadar magungunan da muke siya. Ina amfani da Glucophage na kamfanin Metformin da Daonil kuma suna min aiki a jikina.

“A watan Satumba na sayi maganin kan Naira dubu 2 ko da dari biyu, ya danganta da shagon maganin, amma zuwa watan Oktoba ya cilla daga Naira dubu 2 zuwa Naira 6,500,” inji shi.

Ya ce hakan ne ya sa ya rage yawan magungunan da yake amfani da su musamman Multi-Vitamin da Biobetic da Biopentin wanda ake sayarwa a dubu 5 maimakon dubu 3.

Shi ma da yake jawabi, wani mai dauke da ciwon sugan mai suna Igbinovia ya ce yana shan wuya sosai kan tashin farashin magungunan.

“Mafi saukin maganin ciwon suga shi ne Dabetimi wanda yanzu shi ma ya koma naira dari 4 maimakon dari 3 a watan Oktoba.”

Ya ce wasu lokuta yakan koma wa maganin gargajiya ne idan magungunansa suka kare kuma ba shi da kudin sayen wasu.

Ya yi kira ga Gwamnatin Tarayya da ta sanya tallafi kan magungunan ciwon suga inda ya ce mutane da dama na mutuwa da wannan ciwon saboda rashin halin sayen magungunan.

Shi ma Daniel Edegbe, wani mai sayar da magunguna ya ce rashin jarin shigo da magunguna da hauhawar farashin dala da musayan kudin kasashen waje da karin farashir man fetur sun taimaka wajen ficewar kamfanonin magunguna daga kasar nan.

“A watan Satumban bana ana sayar da miligram 500 na Glucopage a kan Naira 1,000 amma yanzu ana sayar da shi ne a Naira 1,500 kowane kwali.

“Shi kuma fakitin milgiram 1,000 da ake sayarwa a kan Naira 4,500 a watan Agusta, ya haura zuwa Naira 6,200 a watan Satumba.

“Farashin komai ya tashi har na magunguna. Duk nau’ukan magunguna sun yi tsada. Augmentin da ake sayar da shi kan Naira 700 a watan Agusta yanzu ya koma Naira 2,600 ko fiye da haka,” inji shi.

Da aka tambaye shi ko hakan ya shafi cinikin da ake sai ya ce babu alamar hakan.

Mafita

Shugaban kungiyar PSN, Usifo ya bukaci da a kara kaimi wajen yawaita magungunan da ake sarrafawa na cikin gida, inda ya kara da cewar, “abubuwan da mu ke gani ya zamar mana bakon lamari sai dai kuma hakan ya kara bude mana idon ganin hakikar al’amura a yadda suke.

“Wannan wata dama ce a gare mu don dogaro da samar da magungunanmu na cikin gida.”

Umaru Abdulkareem, shugaban kugiyar PSN ta jihar Borno ya kuma shawarci jama’a da su rika sayen magungunan sauran kamfanonin da suka yi rajista da Hukumar Kula da Ingancin Abinci da Magunguna ta Kasa (NAFDAC) sannan su rika kula tare da tantance ingancin irin abincin da za su rika mu’amala da shi idan ba su samu irin wanda aka zayyana musu ba.

Yace: “Idan ba za ka iya sayen masu tsada ba kamar magunguna irinsu Augmentin, akwai wasu na kasa da shi da za ka iya saya su ma suna da kyau kuma ba samfurin kamfanin GSK ba ne.

“Ya kamata gwamnati ta duba yiwuwar karfafa wuraren sarrafa magunguna na cikin gida.

“Matukar ana yin magungunan a cikin gida Nijeriya to za mu iya yin iya kokarinmu wajen daidaita farashin da kuma rage kudinsu.

“Ina kuma shawartar gwamnati da ta yi duk abin da ya dace don saita farashin Dala a kasuwa.”

Ya shawarci ’yan Nijeriya game da su guji zuwa wajen jabun masu ba da magunguna ko masu maganin gargajiya don neman mafita, inda ya kara da cewa, “idan kana da wata lalura ko wata cuta, to ka tafi asibiti su gwada ka sannan kwararru su rubuta maka magunguna.

 

Daga Ojoma Akor (Abuja) da Abiodun Alade & Abdullateef Aliyu (Lagos) da Usman A. Bello (Benin) da Mumini Abdulkareem (Ilorin) da Olatunji Omirin (Maiduguri) da Adenike Kaffi (Ibadan) da Ahmed Ali, Kafanchan.