Wata tirela dauke da dabbobi wacce ta taso daga garin Wudil ta faɗi a shatale-talen Gadar Muhammadu Buhari da ke unguwar Hotoro a Jihar Kano.
Daya daga cikin fasinjojin tirelar, Hashim Rabi’u Tamburawa Gabas ya tabbatar wa Aminiya cewa har yanzu ba su da masaniyar abin da ya sanadiyyar faɗuwar motar.
- ‘Yan sanda sun kama matashi kan zargin satar Naira miliyan 120
- MURIC da FOMWAN sun nemi a hukunta faston da ya raunata liman da iyalansa
Hashim ya shaida wa Aminiya cewa babbar motar ta taso ne daga Wudil inda suka nufi Inugu da Abiya da ke kudancin Nijeriya.
Ya ce bayan zuwansu kan gadar sai dai suka ji motar ta yi ƙara inda ta kife da dukkan kayan da ta ɗebo wanda ya haɗa da shanu da tumaki da albasa da sauran kayayyaki da fasinjoji masu yawa.
Sannan ya ƙara da cewa, ba su da masaniyar abin da ya jefar da motar sai dai suna tunanin ko burkin motar ne ya bawa direban matsala.
Tuni jami’an ’yan sanda ke kusa da wurin da abin ya faru suka kai dauki, inda aka garzaya da wadanda suka jikkata zuwa Asibiti Sa Sanusi da ke unguwar ta Hotoro domin samun kulawa.
Aminiya ba ta samu jin ta bakin jami’in hulda na rundunar ’yan sandan Kano, Abdullahi Haruna Kiyawa dangane da lamarin ba har zuwa lokacin hada wannna rahoto.