Dokta Mariya Bunkure wadda ta maye gurbin Maryam Shetty daga Jihar Kano ta zama Ƙaramar Ministar Birnin Tarayya a Gwamnatin Shugaba Bola Tinubu.
Aminiya ta lurar cewa shugaba kasan ya kuma ƙirkiro sabbin ma’aikatu, ciki har da ta Iskar Gas a sauye-sauyen da ya yi wa ma’aikatun da ya nada ministoci a daren Laraba.
- Matan Kano sun gudanar da addu’o’i kan matsalar tsaro da tsadar rayuwa
- Tinubu ya nada Badaru Ministan Tsaron Najeriya
Da haka Tinubu ya cire kula da harkokin iskar gas daga ƙarƙashin Ma’aikatar Albarkatun Man Fetur.
Yanzu albarkatun iskar gas da na man fetur kowannensu zai kasance a ƙarƙashin kulawar ƙaramin minista.
Haka na zuwa ne a yayin al’amarin tsadar mai ke ƙara ci wa ’yan Najeriya tuwo a ƙwarya bayan cire tallafi, wanda ya sa gwamnatin alkawarin tallafin N8,000 ga matalauta na tsawon wata shida.
Gwamnatin Tarayya ba ta bayyana wanda zai kasance cikakken ministan man fetur ko na iskar gas ba, amma gwamnatin da ta gabata, shugaba Muhammadu Buhari, da kansa ne ya kasance ministan man fetur.
A cikin sauye-sauyen da Tinubu ya yi kuma ya nada ministoci biyu a Ma’aikatar Tsaro (cikakken minista da ƙaramin minista), wanda shi ne karon farko tun bayan dawowar Najeriya kan tafarkin dimokuraɗiyya a shekarar 1999.
Shugaba Tinubu ya kuma ƙirkiro Ma’aikatar Yaki da Talauci, wadda bisa alamu za ta maye gurbin ma’aikatar agaji da ayyukan jin ƙai.
Sai kuma Ma’aikatar Raya Al’adu wadda za ta kasance a ƙarƙashin jagorancin Hannatu Musa daga Jihar Katsina a matsayin minista.
Ya kuma Fada Ma’aikatar Lafiya zuwa ta Walwala da Kula da Lafiya.
Sauran sauye-sauyen sun hada da Ma’aikatar Kasafi da Tsara Tattalin Arziki da aka cire daga Mai’katar Kudi, Kasafi da Tsare-tsare.
Akwai kuma sabuwar Ma’aikatar Matasa da Cigaba sai kuma Ma’aikatar Sufurin Jiragen Ruwa da Tattalin Arziƙin Saman Teku.
A ranar Litinin za a rantsar da ministocin a Fadar Shugaban Kasa da ke Abuja.