A safiyar Alhamis Gwamnatin Tarayya za ta yi sulhu tsakanin Kungiyar Kwadago ta NLC da Gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufai kan yajin aikin kungiyar saboda sallamar ma’aikata 7,000 da El-Rufai ya yi.
Ta kira bangarorin zuwa teburin shawara a Fadar Shugaban Kasa ne bayan kwana uku NLC tana yajin aikin da ya tsayar da harkoki a Jihar, yayin da ake cacar baki tsakaninta da El-Rufai wanda ya ce sallamar ma’aikatan ya zama tilas.
- Gwamnatin Tarayya ta shiga rikicin ’yan kwadago da El-Rufai
- ’Yan daba sun kai wa ’yan kwadago samame a Kaduna
“Mininstan Kwadago da Ayyuka, Chris Ngige ne zai jagoranci zaman sulhu tsakanin Gwamna El-Rufai da NLC,” wanda Ayuba Wabba zai jagoranci bangaren kwadago a wurin zaman a Abuja, a cewar kakakin Ma’aikatar, Charles Akpan.
NLC ta tsagaita wuta
Bayan gayyatar NLC ta dakatar da yajin aikin gargadin kwana biyar din da fara tare da zanga-zangar lumana a Jihar Kaduna, wanda El-Rufai ya ce babban laifi ne, ya kuma lashi takobin yi wa Wabba da sauran shugabannin kwadago abin da sai shiga Jihar zai gagare su.
NLC ta ce ma’aikata za su dakatar da yajin aiki da kuma zanga-zangar lumanar kwana biyar din ne domin ta ga abin da tattaunawar da Gwamnatin Tarayya ta kira tsakaninta da El-Rufai zai haifar.
Zuwa daren Laraba, babu tabbaci game da ko bangaren Gwamnatin Jihar Kaduna za ta amsa goron gayyatar da Ministan Kwadagon ya kira tsakaninta da ’yan kwadago.
Sai Kaduna ta gagari Wabba —El-Rufai
Gabanin haka, ya yi alkawarin tukwici mai gwabi da wanda ya kawo masu Wabba da sauran shugabannin kwadago da ya sanar cewa Gwamnatin Jihar Kaduna na nemansu ruwa a jallo.
El-Rufai wanda ya yi zargin yajin aikin da zanga-zangar makarkashiya ce ga tattalin arzikin jihar ya kuma sanar da korar daukacin ma’aikatan jinyar da ke kasa da mataki na 14 a Jihar saboda sun shiga yajin aikin.
Ya kuma yi barazanar korar duk ma’aikacin da bai je wurin aiki ba a lokacin yajin aikin, amma kungiyoyin da ke karkashin inuwar NLC a jihar suka ci gaba da tsunduma yajin aiki.
Kura ta fara lafawa
Yanayin da aka shiga ya kai ga kungiyoyin da ke karkashin NLC a Najeriya sun fara zaman shirin ko-ta-kwana na shiga yajin aikin gama gari a fain Najeriya, a yayin da su da masu fada a ji ke shawartar El-Rufai da ya bi a hankali kada lamarin ya dagule.
A halin yanzu dai kusan daukacin kungiyoyin ma’aikata a Jihar sun shiga yajin aikin da NLC ta kira, wanda ke neman rikidewa ya koma na gama-gari a fadin Najeriya.