✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Yadda tattalin arzikin Najeriya ya kara tsukewa

Faduwar tattalin arzikin Najeriya ya ninka hasashen Bankin Duniya

Tattalin arzikin Najeriya yana fuskantar barazana sakamakon faduwar da kashi 6.10 cikin 100 a zango na biyu na shekarar 2020.

A rahoton da da Hukumar Kididdiga ta Kasa (NBS) ta fitar, ta ce tsukewar tattalin arzikin zai kawo karshen murmurewar da tattalin arzikin da Najeriya ke yi tun matsin tattalin arzikin da ta fada a 2016/2017.

A ranar 25 ga watan Yuni 2020, Bankin Duniya fitar da bayanin cewa Najeriya za ta shiga mafi hadarin koma bayan tattalin arziki sakamakon karyewar farashin man fetur da annobar COVID-19.

A hasashen Bankin Duniyar, za a samu faduwar kashi 3.2% cikin dari na tattalin arziki cikin 2020, amma sai Najeriya ta buge da kashi 6.10%.

NBS ta alakanta faduwar da tattalin arzikin da raguwar huldodin kasuwancin kasar — na gida da na waje — suka samu a zango na biyu na 2020 sakamakon COVID-19 da ta sa aka rufe kasar.

Ta ce hana zirga-zirga tsakanin jihohi da hana shige da fice na kasa da kasa da dokar hana kulle da kuma rufe makarantu da kasuwanni sun kara nakasun.

“Kokarin da gwamnatocin jiha da na tarayya suke yi a tsawon watanni farkon na shekara sun taimaka”, inji hukumar.

Idan ka yi la’akari da yanayin tattalin arziki a zango na biyu na shekarar 2019, an samu karin kashi 2.12%.

An kuma samu faduwar kashi 8.22% a zango na biyu na shekarar 2020, da kuma faduwar kashi 7.97% idan aka kwatanta da zangon farko a shekarar 2020 (1.87%).

Darajar kayan da ake samarwa a cikin gida (GDP) a zangon farko na 2020 ya ragu da kashi 2.18% sabanin kashi 2.11% a zangon farko na 2019.

Faduwar da aka samu a darajar kayan da Najeriya ta samar a zango ne kashi 5.04% ne.

Wani bayani kuma ya yi nunin cewar darajar kayan da ba fetur ba sun fadi da kashi -6.05 a cikin kashi 1.55 na zango farko na shekarar 2020, sai kuma kashi 1.64 cikin dari na zango farko a shekarar 2019.