✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda taron Muryar Talaka karo na 7 ya gudana a Kwantagora

A ranakun Juma’a da Asabar da suka gabata ne kungiyar Muryar Talaka ta gudanar da babban taronta na shekara-shekara karo na 7 a Kwantagora, Jihar…

A ranakun Juma’a da Asabar da suka gabata ne kungiyar Muryar Talaka ta gudanar da babban taronta na shekara-shekara karo na 7 a Kwantagora, Jihar Neja.

Bayan shirya wa ’ya’yan kungiyar da sauran baki da suka zo daga sassan Najeriya da wasu kasashen Afirka da shugabannin kungiyoyin Miyetti Allah  da na Zavi Sonka ta kasa da  na Kontagora Frontiers Forum  liyafar musamman, Shugaban kungiyar ta kasa, Zaidu Bala kofa Sabuwa ya bayyana nasarorin da kungiyar ta samu a tsawon shekaru, inda ya ce nasarar ba tasa ba ce shi kadai, ta kowa da kowa ce. Sannan ya bukaci ’ya’yan kungiyar su kara kwazo don ci gaban al’umma.

Shugaban ya kuma jagoranci wata ziyara zuwa fadar Mai martaba Sarkin Sudan na Kwantagora, Alhaji Sa’idu Namaska, tare da shugaban kungiyar a Jihar Neja, Alhaji Murtala Maigyada Kwantagora da uban kungiyar, Ministan Matasa da Wasanni, Barista Solomon Dalung wanda Alhaji Maiwada danmalam ya wakilta da sauran mambobin kungiyar. 

Alhaji Zaidu Bala ya shaida wa Sarkin  cewa sun je fadar ce domin neman albarka bisa al’adar kungiyar na ziyartar iyayen kasa a duk jihar da suke taro, saboda muhimmancinsu, sannan ya yi fatan Allah Ya kara wa Sarkin lafiya.

A jawabin Sarkin, wanda Madakin Kontagora ya wakilta ya nuna goyon bayansa ga kungiyar, kuma ya ce sun dade suna jin sunanta, sai a wannan lokaci suka samu haduwa da shugabanninta.

An gabatar da jawabai da mukaloli daga manyan baki kan kalubalen da ke fuskantar Najeriya da suka hada da Dokta Isa Adamu daga Jami’ar Ibrahim Badamasi Babangida da ke Lapai,da Dokta Muhammad Ibn Imam daga Kwalejin Ilimi ta Tarayya da ke Kwantagora da Fasto Yohanna Buru daga Kaduna da kuma Dokta Aliyu Muhammad Muri daga Katsina.

Taron ya kuma karrama wadansu fitattun mutane irin su Limamin Kwantagora da wakilin Sarkin Sudan na Kwanatgora da kuma gwarzon shekara na kungiya, Alhaji Abdurrahman Buhari MK, wani hamshakin attajiri da ke taimaka wa talakawa. Saura sun hada da Ajiyan Kwantagora, Alhaji Mamman Ajiya, da Mukaddashin Darakta Gidan Rediyon Jihar Neja, Injiniya Rabi’u Idris SB da dan Majalisa mai wakiltar Agwara, Barista Bello Ahmad. Sai Barista Solomon Dalung, wanda babban hadimin ofishinsa Alhaji Maiwada danmalam ya wakilta. 

A karshe kuma ayarin ’yan wasa da suka hada da Washasha Group daga Katsina da Ahmed Ekualizer daga Zamfara da ’yan wasan tauri daga Kwantagora duk sun nishadantar da mahalarta taron.