Sojoji sun tarwatsa wata maboyar ’yan ta’adda tare da kama masu kungiyar tayar da kayar baya 410 ta Darul Salam a Jihar Nasarawa.
Rundunar soji ta Operation Whirl Stroke da ke aikin samar da tsaro a yankin Arewa ta tsakiya ta ce ta kuma kwato kona masana’atar makamai tare da kwace ababen fashewa da sauran makamai a maboyar ’yan kungiyar.
Kakakinta, Manjo Janar John Enenche ya ce mutanen da aka kama ’yan kungiyar Darul Salam ne da suka hada da mata da kananan yara a Karamar Hukumar Uttu ta jihar.
Ya ce sojoji an kama mutanen da tarwatsa masana’antar ababen fashewarsu ne bayan tattara bayanan sirri a kokarinsu na kakkabi yankin daga miyagu.
A cewarsa sun gano ababen fashewa na gida masu tarin yawa da suka hada da bama-bamai, baya ga rokoki da sauran makamai masu hadarin gaske da kirar gida.
Janar Enenche ya ce dakarun sun kona mafakar kungiyar bayan tsare mutanen da kwashe makaman yayin da take bin sawun wadanda suka tsere.