Rundunar Sojin Kasa ta Najeriya ta tabbatar da kashe dan ta’addan da ake nema ruwa a jallo a Jihar Binuwai, Terwase Akwaza, wanda aka fi sani da Gana.
Kwamandan Runduna ta musamman mai lamba hudu a Jihar Nasarawa, Manjo Janar Moundhey Ali, ya ce an kashe Gana ne a wani shingen bincike na sojoji a kan hanyar Gbese-Gboko-Makurdi, bayan musayar wuta wuta da ’yan bindiga.
- Sojoji sun bindige kasurgumin dan ta’ddan Binuwai
- Sauye-sauyen da aka yi wa Masarautun Kano
- ‘Yan sanda sun mika Naira miliyan hudu da aka tsinta a mota
“Yau (Talata) mun samu bayanan siriri game da tafiya Terwase Akwazwa Agabu (Gana) a kan hanyar Gbese-Gboko-Makurdi.
“Nan take dakarun Rundunar ‘Ayem Akpatuma III suka kafa shingayen bincike a kan hanyar.
“Da misalin karfe daya da rana aka yi arangama da tawagar Gana, inda aka yi musayar wutar aka kuma kashe shi”, inji Janar Ali.
Kwamandan ya ce sojoji sun damke 40 daga cikin yaran Gana a lokacin artabun, kuma za su mika su a hannun hukumomin da suka dace domin gurfanarwa a kotu.
Ali ya ce an kwace manyan bindigogi iri-iri da albarusai da ababen fashewa da kuma da layu daga hannun ’yan ta’addar.
Ya kuma ce gawar Gana na ajiye a wani asibiti da bai bayyana ba.
A shekarar 2015 Gwamantin Jihar Binuwai ta yi afuwa ga wasu mutum 500 cikinsu har da Gana, masu addabar jihar da makwabciyarta ta Jihar Taraba.
Sai dai daga baya yawancin mutanen da aka yi wa afuwar sun koma ’yar gidan jiya.
Daga baya a 2017 ’yan sanda suka ayyana Gana a matsayin wanda ake nema ruwa a jallo kuma Gwamnatin Jihar Binuwai ta sanar da tukwicin Naira miliyan 10 ga duk wanda ya kawo bayani a kan inda yake.