✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Yadda Sheikh Dahiru Bauchi ya yi bude-baki tare da fastoci

Fastoci daga jihohi 19 na Arewacin Najeriya da malaman Musulunci sun yi bude-baki a gidan shehin malamin.

Tawagar fastocin jihohi 19 na Arewacin Najeriya sun ziyarci Gidan Shaikh Dahiru Bauchi domin yin bude-baki tare da shehin malamin da sauran malaman Musulunci da ya karbi bakunci.

Fastocin, karkashin jagorancin Fasto Yohana Buru na Cocin Christ Evangelical and Life Intervention Ministry, da ke Jihar Kaduna sun ziyarci shehin malamin ne domin kara yaukaka dangantaka a tsakanin Musulmi da Kiristocin Najeriya.

A cewar Fastor Yohanna, “Mun zo bude-baki a azumin Ramadan ne tare da ’yan uwanmu Musulmi a gidan Sheikh  Dahiru Bauchi ne domin inganta fahimta.

“Fiye da shekara 11 ke nan muke gangamin neman zaman lafiya musamman lokacin Iftar domin mu kara fahimtar junanmu da malamai;

“Ciki har da Sarkin Musulmi, Muhammad Sa’ada Abubakar, Sheikh Ibrahim Yakub El-Zakzaky, Sheikh Dahiru Bauchi, Sheikh Salihu Mai-Barota, da Sheikh Mohammed ibn Abdul a Jihar Neja.

“Har da wasu malaman da ke makwabtan kasashe irin su Jamhuriyar Nijar da Jamhuriyar Benin domin yin wa’azi a kan muhimmancin zaman lafiya da fahimtar juna a tsakaninmu,” inji shi.

Ya kara da cewa, “Kiristoci da Musulmi Allah ne Ya halicce su kuma dukkan addinan na da litattafai da aka saukar musu, dukkanmu ’ya’yan Annabi Adam ne, don haka akwai bukatar fahimtar juna.”

Da yake jawabi, Sheikh Dahiru Bauchi ya nuna farin cikinsa ga ziyarar da fastocin suka kai mishi da kuma kokarinsu na yada zaman lafiya a Najeriya.

Ya jaddada bukatar ci gaba da yi wa kasa addu’a domin a samu a magance matsalolin da suka yi wa kasar katutu a yanzu, sannan ya shawarci Musulmi da Kiristoci da su ci gaba da zama lafiya da juna.