✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda Shata ya nada ni Sarkin Kanon ’yan mota – Sarki Labaran

Alhaji Sarki Labaran Abubakar ya shahara a sanadiyyar wata waka da Shata ya yi masa mai taken “Sarki mijin ‘yar Sarkin Labaran,” kuma mutum ne…

Alhaji Sarki Labaran Abubakar ya shahara a sanadiyyar wata waka da Shata ya yi masa mai taken “Sarki mijin ‘yar Sarkin Labaran,” kuma mutum ne wanda ya sahahara a tsakanin direbobin da. Don haka Aminiya ta ziyarci gidansa inda ya yi bayanin yadda Marigayi Alhaji Dokta Mamman Shata Katsina ya nada shi ‘Sarkin Kanon ’yan mota’ a cikin wakar,’ da yadda ya sha gwagwarmayar rayuwarsa, tun daga siyasar NEPU da harkar tukin mota da sana’ar da ya koya a karkashin mahaifinsa. Ga dai yadda hirar ta kasance:

Aminiya: Alhaji ko za ka bayyana wa masu karatu takaitaccen tarihin rayuwarka?
Sarki Labaran: Ni dai ba zan iya tuna shekarar da aka haife ni ba, amma ina jin zan dan haura shekara 74. Kuma gata irin na da ya sa aka katse karatunmu, domin na yi kwatankwacin Firamare, inda aka cire ni ina da shekara 12; sannan na sauke Alkur’ani ina da shekara 15. Abin da ya sa na ce maka gata ne ya sanya aka cire ni daga makaranta shi ne, a da kamen mutane ake yi don su shiga makaranta, kusan komai kyauta ne. Kai asibiti ma kyauta ne a lokacin, domin motar asibiti ana yi mata lakabi da “Allah Ya isa.” Bayan da aka yi mana wannan gata, sai na rika yin sana’ar mahaifina, wato saukar baki; na kuma rika zuwa wajen abokin mahaifina Alhaji danwawu Fagge ina sayen bakaken tufafi, wato rigar baki “ta kore.” A haka, a haka, har muka koyi sana’a. Da girma ya zo mana sai aka ba mu jari, inda na rika sayen tsofaffin tayoyin keke ina yin takalman taya, wato fade, irin wadanda Fulani ke sanyawa. Haka na yi ta kai kawo daga kasuwar Kurmi zuwa Dandalin Fage, wajen Zakari dangata da Sharu Angale da Alhaji Ado Gurufa da Cibayo.
Aminiya: Wato ka fara cin gashin kanka a sana’a ke nan?
Sarki Labaran: E, ina kuma taba siyasar NEPU. Domin wadancan mutane da ka ji na ambata, wato Ado Gurufa da Cibayo, ai tsokana ce. Su ’yan NEPU ne, amma ba su kaunar a hada su da NPC ko ’yan doka, shi ya sa aka yi musu lakabin Gurufa da Cibayo, ma’ana Gurufa “dan jam’iyyar NPC,’ shi kuwa Cibayo ana nufin “dan doka” ke nan.
Aminiya: Yaya aka yi ka tsunduma a harkokin siyasar NEPU?
Sarki Labaran: Rigingimun siyasa suka sanya muka je gidan Sarki Sanusi, lokacin ana kara masa girma, nan da nan aka kama mu aka tsare, wai saboda jar hularmu, ita ce ka ga Gwamnan Kano na yanzu Kwankwaso yana kwaikwayo, amma tamu ta sha bamban da tasa.
Allah dai Ya kwato mu, bayan mun shafe mako guda a kurkuku. Iyaye suka bi ta hannnun manya, aka kuma yi ta yin addu’a. Don haka da aka zo kanmu a wajen shari’a, sai Sarki da kansa ya ce, wadannan ba su ma isa shari’a ba. Sai aka sake mu.
Bayan da muka fito, sai aka fahimci na iya karatu da rubutu, don haka aka ba ni Shugaban wata kungiya da Malam Aminu Kano ya bullo da ita, wato Zaharal Hakku Al’umm Faukal Hukuma, ma’ana “gaskiya ta bayyana, Jama’a su ne gaba da Hukuma.” Ina cikin harkokin wannan kungiya, sai fargabar ’yan NEPU ta far mana, a lokacin da ake ta kamensu, sai na yi gudun hijira zuwa kasar Saliyo. An yi ta addu’a, har na dawo, aka zauna lafiya. Sai na koma sana’ar takalmin danko da saida tsohuwar taya.
Aminiya: To ya aka yi ka shiga harkar tukin mota har ka shahara?
Sarki Labaran: A da babu tashar mota irin tamu ta jakara, don haka mahaifin Alhaji Sulen Garo, wato Galadiman Garo, idan suka zo da motarsu, sai su je gidanmu su huta, har sai fasinja sun cika, su dauka su tafi. Sai Allah Ya hada ni da Garba dan Galadiman Garo, kanen Sulen Garo, inda Allah da ikonsa shi ya nuna mini miota da direbansu, suka cusa mini sha’awarta. Bayan sun cusa mini soyayyar mota, sai mota ta shiga raina. Allah cikin kudurarsa, sai aka sayi mota a gidanmu, na zama akawunta. Ana nan mota ta janye dukkan harkokina, har na zama mai tukata.
Aminiya: Yaya aka yi kuka hadu da Alhaji Mamman Shata har ya yi maka waka?
Sarki Labaran: Haduwarmu da Shata bai fi shekaru biyu da fara tukina ba, wato a shekarar da aka yi bikin ’yan sarki (1954). Kodayake a lokacin ba mu isa mu je wajensa ba. Soyayyarsa ta shiga zuciyarmu, har Allah Ya kawo Abu Darma, muka yi abota da shi; shi dan Katsina ne, kuma mahaifinsa sun saba da Shata. Wata rana sai ya dauke mu muka tafi Katsina, Shata na wasa, sai ya kai mu wurinsa, a haka muka saba da shi. A lokacin ana kirana Sarkin Kano saboda da siyasa, amma da Shata ya tashi yi mini waka, sai ya mayar da ni “Sarkin Kanon ’yan mota.”
Aminiya: a wacce shekara shata ya yi maka waka?
Sarki Labaran:Ina kyautata zaton a shekarar 1968 ne, domin a lokacin aka kama ni, ni da motar muka shiga soja. An kama mu a tashar Kaduna, muna ta yin aikin soja, inda na zama wurin ajiyar kaya “motata ita ce store.” Ba a sake mu ba har bayan yaki a shekarar 1972. Muna da yawa, wadanda aka kama, zan dai iya tuna Alhaji Hussaini Gumel da Gambo dan-ifiritu da Idi Ka-mari Duwan.Sarki Labaran  (a tsakiya) lokacin yana shugabancin qungiyar samarin NEPU ta Gaskiya ta bayyana a shekarar 1954Aminiya: Wacce kyauta ka yi wa Shata ta burge shi har ya yi maka waka?
Sarki Labaran: Ai kasan shi Shata kyautarka ko yawan kudinka ba sa burge shi. Kawai idan ya ga dama, mai kudi kadan sai ya burge shi, ya yi masa waka, ya kuma ki yi wa mai kudi da yawa. Abubuwa biyu da nike iya tunawa sun burge Shata game da ni, su ne, Ya je neman motoci da zai yi haya zuwa Funtuwa, don an yi masa haihuwa, sai aka ki yi masa sauki, shi kuwa wanda motocin ke hannunsa Nuhu Jikan Sarki sai ya sanar da ni. Da muka je wurin mai motar a Zariya muka nuna masa ni nike son motocin sai ya yarda ya yi mini ragi, sai na biya, muka zo muka gaya wa Shata. Ni kuma na ce da shi wane waje kake son a kai motocin, ni na tafi da tawa, Liman ya tafi da tasa. Da ya bai wa Nuhu kudin, sai na ce a mayar masa na riga na biya. Aka mayar masa da kudin. Ya dade yana godiya. Muka je aka sauke mu a Otal din Hamdala da ke Funuwa, su Abu Darma suka zo suka same mu. A nan ne wakata ta zama “Sarki mijin ’yar Sarki Labaran.” Sai kuma rigimarmu da mutanen Funtuwa. Da shi Shata ya ce kyauta za a shiga wasa, kuma Maude (Tabako) ya bayar da kayan kidan Neja a yi amfani da su kyauta. Ni kuwa na ce sai an sanya kudin shiga, ko da kadan ne, sai wani Bakatsine ya zo yana zage-zage, ‘wai Kanawa mun cika son kudi; mu barayi ne.” muka ce masa mu masu nema ne. Mu da kake ce wa son kudi. Sai na fito da bandir din Fam 500 na jika 25 na ce wa abokin rigima ya fadi kudin gidansu, in biya, in bai wa waccan matar kyauta (na nuna wata tsohuwa). Ashe Shata ya ga abin da ya auku, don haka a wakata ya kara da cewa, ‘bindiga mai dadin sababi.’
Kyauta ta biyu kuwa, na sayi wadansu motoci a gwanjo na bayar a sayar da daya a ’Yan-bahed, shi kuwa Shata ya zo ya taya bai san tawa ba ce; kuma aka ki sayar masa. Daga baya ya ji cewa tawa ce; ni kuma da aka bayyana mini, da na ji sai na bari lokacin da ya zo Kano, zai yi wasa da La’asar a Kissgadi (King’s Garden), kuma wasan ana yi masa lakabi da wasan kirikiri, sai na zo waje ya cakude. Sai na ce a yi he, aka ce he! A gaya wa Shata motar da ya taya, ya je ya kai musu la’ada ya karbo; ga takardunta nan na ba shi. Har bincike ya rika yi ni dan wane ne, a wuraren da ake taruwa.
Da muka hadu da Shata a bikin Hamza Habeeb, wanda ya auri diyar ministan Sardauna, da kansa ya aiko cewa kada in bayar da kudi.
Aminiya: Wacce daukaka kake ganin wakar Shata ta kawo maka?
Sarki Labaran: Al’amuran suna da yawa, amma dai  na san har daga Yammai an hawo mota an zo Kano don a ganni. Kuma wata rana mun fito daga Nijar, ni da Ummaru dandanduna da Liman Na ’Yalleman, mun shigo Gumel ana tsoron wani dan sanda wai shi Hussaini, sai ya tare hanya. To, ni na yiwo lodi, su kuwa ba su dauko komai ba. Nan take ya tsare mu, a daidai lokacin Sarkin Gumel, Baban na yanzu, Alhaji Muhammadu Sani, ya zo wucewa, sai ya ga an yi taro an kewaye mu, sai ya tambaya, me ke faruwa? Aka ce da shi yaran nan ne da Shata ke yi wa waka\, wato da Ummaru dandanduna da Sarki Labaran da Liman na ’Yalleman. Sai Sarki ya zo, ya ce ku ne yaran da ake yi wa waka, to Allah Ya yi muku albarka. Daga nan aka kyale mu muka wuce.
Aminiya: Ko a ganinka za a samu mawaki mai basira irin ta Shata a wannan zamanin?
Sarki Labaran: To baiwar Allah ba ta karewa, amma dai Shata yana da wata karama da ba kowane mawaki ke da ita ba, wato tsara waka nan take; su kuwa saura sai sun yi gwaji a gida kafin su shiga fage. Kuma idan ya fadi magana sai a yi ta mamaki. Domin a wakar da ya yi mini ya fada cewa: Allah Ya jikan Gwaggwagon Labaran, Allah Ya jikan Baban Labaran, har sun mutu bai saba musu ba. Kuma yanzu babu Shata, babu dankwairo, babu Jankidi, ko sarauta ka yi, babu wanda zai yi maka waka. Shi kuwa Shata da an ce ‘he!’ idan aka fadi sunan mutum nan take zai wake shi, idan ma wakarsa ta ki yiwuwa shi kadai, sai a soko shi a cikin Bakandamiya.