Kungiyar Jama’atu Izalatil Bid’ah Wa’ikamatis Sunnah ta kasa da ke karkashin jagorancin Sheikh Muhammad Sani Yahaya Jingir, ta dakatar da dukkan makarantunta na Najeriya da suke dauke da dalibai sama da miliyan bakwai.
Kungiyar ta dakatar da makarantun nata ne, a wata sanarwa da ta fitar wadda ke dauke da sanya hannun Shugaban kungiyar na kasa, Sheikh Abdul Nasir Abdulmuhyi.
Har’ila yau sanarwar ta bayyana cewa, kungiyar ta dakatar da karatun makarantar horar da Limamai da Alkalai da ake gudanarwa yanzu a garin Jos, da taron karawa juna sani na kasa da kungiyar take gudanarwa a kowace shekara.
Sanarwar ta bayyana cewa, kungiyar ta dauki wannan mataki ne, sakamakon bullar cutar annobar coronavirus da ta addabi duniya, kuma ta dakatar da dukkan al’amuranta.
Kungiyar ta tabbatarwa da gwamnati cewa za ta ci gaba da bin dukkan wata doka da gwamnati ta gindaya, kamar yadda ta saba.
Kuma ta yi umarni da a dinga amfani da dukkan shawarwari da gwamnati da masana kiwon lafiya suka bayar kan wannan annoba, domin ganin an dakatar da yaduwarta.
Ta bukaci al’ummar musulmi su dage da addu’o’i tare da komawa ga Allah kan wannan annoba.
Ta yi kira ga gwamnati ta tallafawa marasa karfi a wannan lokaci, domin rage musu radadin zama a gida da suke yi a halin yanzu.