✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda Shagon Alabo ya kashe Bahagon Lauwali

A ci gaba da damben gargajiya da ake fafatawa a gidan dambe na kasuwar Alaba Rago, a makon da ya gabata Sama’ila Shagon Alabo na…

Sama’ila Shagon Alabo ya take dambe da Bahagon Lauwali a gidan wasan dambe na Alaba Rago. A ci gaba da damben gargajiya da ake fafatawa a gidan dambe na kasuwar Alaba Rago, a makon da ya gabata Sama’ila Shagon Alabo na bangaren kudu ya yi wa Bahagon Lauwali na bangaren guramada kisa daya mai ban haushi.
Damben wanda ya gudana a gidan dambe na Alaba Rago ya kayatar kwarai da gaske domin yadda ’yan damben suka nuna kwarewarsu a fagen wasan.
Sama’ila Shagon Alabo ya sami nasara ne a turmi na biyu bayan da suka fafata a turmi na daya babu wanda ya yi kisa.
Mai horar da su kuma kwararre a hakar dambe mai suna Malam Muhammadu Maizube ya bayyana cewa Shagon Alabo sa’a kawai ya samu.
‘Domin Bahagon Lauwali ya ba shi wahala kwarai da gaske. Kisan ne kawai ya zo ta hannun Shagon Alabo amma ba don haka ba da wasa ya sauya. Da farko mutane sun yi zaton Bahogon Lauwali ne zai yi kisa saboda irin bugun da ya rika kai  masa’. In ji shi.
Maizube wanda dan asalin kauyen Takai ne a Jihar Kano ya bayyana cewa kisan ya zo ne lokacin da suka rukume juna suna bugun junan su. ‘Suna cikin yin amarya sai Allah ya ba Shagon Alabo sa’a ya daki kan Bahagon Lauwali, sai kawai ya fadi’. In ji shi.
Ya bayyana cewa ba tun yau suka fara dambe a tsakanin su ba don sun jima suna yin dambe a wurare daban-daban. Ya kara da cewa Sama’ila Shagon Alabi shi yake bin Bahagon Lauwali bashin kisa domin ya kashe a wani wuri.