Wata kotun majistare dake zamanta a Abeokuta babban birnin jihar Ogun ta yankewa wani matashi mai suna Afolabi Samuel hukuncin daurin shekara daya a gidan yari bayan samunsa da laifin sata a coci.
Matashin dai mai kimanin shekaru 21 a duniya ya amsa laifin da ake tuhumarsa da shi na satar wasu wayoyi biyu kirar Tecno da darajarsu ta kai kusan N128,000.
- An rufe makarantar da bakuwar cuta ta barke a Sakkwato
- Dole a rika yi wa mahajjata rigakafi ko gwajin COVID-19 duk sati – Saudiyya
Alkalin kotun, Mai Shari’a D. S. Ogongo ya ce kotun ta yanke masa hukuncin ne bayan gamsuwa da hujjojin da aka gabatar a gabanta cewa wanda ake zargin ya aikata laifin.
Daga nan ne sai ya yankewa matashin hukuncin daurin shekara daya a gidan kurkuku ba tare da zabin biyan tara ba.
Tun da farko dai ’yar sanda mai shigar da kara, Insifekta Olaide Rawlings ta shaidawa kotun cewa an aikata laifin ne ranar 24 ga watan Fabrairun 2021 a Cocin Celestial Church of Christ da ke unguwar Ilawo a Abeokuta.
’Yar sandan ta ce matashin ya yi amfani da karfin tuwo ne wajen ballewa tare da shiga cocin ta taga da tsakar dare, sannan ya sace waya kirar Techno Camon-16 wacce kudinta ya kai kimanin N76,000, mallakar wani mai suna Ganiu Adeola.
Ta kara da cewa matashin ya kuma saci wata wayar wacce ita kuma darajarta ta kai kimanin N52,000, mallakar Mista Dairo Theophilus.
Insifekta Olaide ta ce an sami nasarar kamashi ne da taimakon fasahar bibiyar wayar salula.
Ta ce laifin ya saba da tanade-tanaden sassa na 415 da 383 da kuma na 309 (9) na Kundin Manyan Laifuffuka na jihar Ogun na 2006.