Ga dukkan alamu sa-toka-sa-katsi da ke gudana a tsakanin Mai martaba Sarkin Kano Malam Muhammadu Sanusi II da Gwamnan Jihar Dokta Abdullahi Umar Ganduje ya kai matakin tika-tika-tik, bayan da gwamnatin Jihar Kano a karkashin Gwamna Ganduje ta kekketa Masarautar Kano ta hanyar kirkiro sababbin masarautu hudu daga cikinta, inda yanzu jihar ke da masarautu biyar.
Kirkiro masarautun ya tabbata a shekaranjiya Laraba bayan da Gwamna Abdullahi Ganduje ya rattaba hannu a kan dokar kirkiro masarautun da Majalisar Dokokin Jihar ta aike masa .
Masarautar Kano ba za ta taba mantawa da wannan mako mai wucewa ba sakamakon wasu matsaloli da suka dabaibaye masarautar da suka hada da kirkiro sababbin masarautun hudu da kuma ci gaba da binciken masarautar da kuma Sarkin Kano Malam Muhammadu Sanusi II, kan zargin kashe kudi ba bisa ka’ida ba da Hukumar Karbar Korafe-Korafe da Yaki da Rashawa ta Jihar Kano take aiwatarwa.
Masarautar Kano ta fuskanci kalubale daga Gwamnatin Gwamna Abdullahi Umar Ganduje ne sakamakon rawar da ake zargin Sarkin Muhammadu Sanusi ya taka a lokacin zaben gwamnoni da aka gudanar a watan Afrilun da ya gabata.
Ga duk mai bibiyar al’amuran siyasar Jihar Kano musamman a baya-bayan nan, wannan dambarwa ba za ta ba shi mamaki ba, ganin yadda aka sanya zare a tsakanin Sarkin da Gwamna, musamman lokacin da al’amarun siyasa suka kankama a dab da gudanar da zaben Gwamna na bana.
A ranar Litinin da ta gabata ce wani ayarin lauyoyi a karkashin Malam Ibrahim Salisu Chamber, suka gabatar da wata takardar koke a gaban Majalisar Dokokin Jihar Kano suna neman a duba yiwuwar kirkiro sababbin masarautu hudu a jihar.
Ayarin lauyoyin wanda ya bayyana cewa ya gabatar da korafin ne a madadin wata kungiya da ake kira West African Institute for Legal Aid (WAILA), ya nemi a kirkiro masauratun Gaya da Rano da Karaye da kuma Bichi.
Bayan da majalisar ta karbi korafin ne, sai Shugaban Majalisar, Alhaji Kabiru Alhassan Rurum ya karanta korafin a zauren majalisar, inda a sakamakon haka ilahirin ’yan majalisar suka yarda da cewa a karbi korafin kuma a yi nazari a kansa. Nan take aka karbi korafin kuma majalisar ta umarci kwamitinta mai kula da harkokin da suka shafi kananan hukumomi da masarautu ya duba shi, sannan ya hada shi a cikin rahoton da zai mika ga majalisar wanda yake aiki a kansa tun a bara.
Sakamakon haka sai majalisar ta umarci kwamitin ya mika mata rahoton washegari Talata 7 ga Mayun bana. Haka kuwa aka yi, domin a zaman majalisar na ranar Talata, kwamitin ya mika rahotonsa na hadin gwiwa da Kwamitin Kananan Hokumomi da na Shari’a kuma a ciki, ya ba da shawarar cewa zauren majalisar ya amince da duk kudurce-kudurcen da rahoton ya kunsa. Bayan da Shugaban Masu Rinjaye a Majalisar, Alhaj Baffa Babba Dan’agundi ya karanta rahoton kuma wani dan majalisar ya karfafe shi, sai zauren majalisar ya amince da rahoton.
Daga bisani Shugaban Majalisar ya nemi ra’ayin ’yan majalisar a kan wannan rahoto kuma mambobi 10 suka tofa albarcin bakinsu a kai. Dukkan ’yan majalisar 10 sun nuna goyon bayansu ga samar da sababbin masartautu a Kano. A cewarsu, yin haka zai samar da gagarumin ci gaba a Jihar Kano kamar dai yadda ake gani a makwabciyar Kano wato Jigawa wacce ke da masarautu guda biyar.
Daga nan ne sai aka yi wa rahoton karatu na daya kuma duk ’yan majalisar suka amince sannan aka dage zaman majalisar zuwa shekaranjiya Laraba domin yi wa rahoton karatu na biyu da na uku.
A shekaranjiya Larabar kamar yadda aka yi alkawari, an yi wa rahoton karatu na biyu da na uku kuma dukkan ’yan majalisar suka amince a kirkiro sababbin masaruatun ba tare da wata takaddama ba.
Sai dai dan majalisa mai wakiltar Karamar Hukumar Dambatta, Alhaji Hafizu Sani Mai Daji, ya fice daga zauren majalisar don nuna rashin amincewarsa ga yadda aka raba sababbin masarautun.
Da yake yi wa manema labarai jawabi, Mai Daji ya ce ko kadan ba a yi wa Karamar Hukumar Dambatta adalci ba, saboda hana ta masaurata. Ya ce Dambatta masarauta ce mai tarihi, hasali ma hakiminta shi ne hakimi mafi yawan shekaru a kan mulki kuma babban dan Majalisar Sarki ne kuma daya daga cikin masu nada sabon sarki, amma duk da haka aka tsallake shi aka kai sarautar garin Bichi.
Bayan da majalisar ta shafe kimanin awanni hudu tana zaman sirri, sai aka dawo cikin zauren, inda shugabanta, Kabiru Rurum ya bayyana sakamakon ganawar sirrin da ’yan majalisar suka yi kuma daga bisani majalisar ta amince da kafa wannan doka ta kirkiro sababbin masarautu hudu a Kano.
Kammala zaman ke da wuya sai wakilin Aminiya ya nemi karin bayani daga bakin Shugaban Masu Rinjaye na Majalisar, Alhaji Baffa Babba Dan’agundi, inda ya ce majalisar za ta mika dokar ga Gwamna Ganduje domin sanya mata hannu ta zama cikakkiyar doka, kuma daga baya Gwamna zai bayyana sunayen mutanen da za su zamo masu nada sababbin sarakunan a sababbin masarautun.
Dan’agundi ya ce, sabuwar Masarautar Bichi za ta kasance ce a karkashin iyalan gidan Malam Dabo, sai masu nada Sarki a Kano a yanzu su ne za su kasance masu nada Sarki a Masarautar Bichi. Kuma ya ce duk wani dan sarautar Masarautar Kano da ya gaji sarauta yana iya shiga takarar neman sarautar Kano koda kuwa ya kasance hakimi ne shi a masarautar Bichi. Ya kara da cewa sai dai sauran masarautun da suka hada da Rano da Gaya da Karaye gwamnati za ta nada musu masu zaben Sarki daban da na Masarautar Kano.
Bayan tashi daga zamansu, Shugaban Majalisar ya jagoranci sauran ’yan majalisar zuwa Gidan Gwamnati domin mika wannan kudiri da sauran wasu daban ga Gwamna Ganduje domin sanya musu hannu su zama dokoki kamar dai yadda Kundin Tsarin Mulki ya tanada.
Tirka-tirka a tsakanin gwamnati a karkashin Gwamna Ganduje da Masarautar Kano a karkashin Sarki Sanusi ll, ta kara tsami ne bayan kammala zaben Gwamna na bana. Hakan ta faru ne sakamakon zargin da ake yi wa Sarki na taka muhimmiyar rawa a lokacin zaben, domin ganin Gwamna Ganduje bai samu nasarar dawowa a matsayin Gwamna ba. Don haka bayan da Ganduje ya samu nasarar lashe zaben Gwamna sai dangantaka a tsakanin Gwamna da Sarkin ta kara tsamari ainun.
Wadansu suna zargin cewa wannan ne dalilin da ya sa gwamnatin Kano ta himmantu don ganin cewa ta karya fika-fikan Sarkin domin rage masa karfi a sarautance.
A can baya gwamnatin ta yi yunkurin cire Sarkin Kano bisa zargin almundahana da dukiyar al’umma ta biliyoyin Naira, sai dai wata majiya ta shaida wa Aminiya cewa sakamakon sa bakin da wadansu fitattun mutane a kasar nan suka yi ciki har da tsofaffin shugabannin kasa, Janar Ibrahim Badamasi Babangida da Janar Abdulsami Abubakar da fitaccen attajirin nan Alhaji Aliko Dangote, sai gwamnatin ta dakatar da wancan yunkuri nata.
Bayan da Shugaban Majalisar da ayarinsa suka kai dokar Gidan Gwamnati a shekaranjiya Laraba, tare da wasu sababbin dokoki guda shida nan take Gwamna Ganduje ya rattaba wa dokokin hannu ciki har da ta kirkiro sababbin masarautu n hudu a jihar inda haka ya nuna amincewar Gwamnatin Jihar Kano kan kirkiro masarautun.
Da yake bayani jim kadan bayan rattaba wa dokar hannu, Gwamna Ganduje ya tabbatar da cewa nan ba da dadewa ba gwamnati za ta bayyana sunayen sarakunan sababbin masarautun kuma ta mika musu shaidar nada su a matsayin sarakuna.Gwamna Ganduje ya kara da cewa gwamnatin za ta sa rana domin gudanar da bikin nade-nadn sarautun sababbin sarakunan nan ba da dadewa ba. Ya ce kirkiro sababbin masarautun wata alama ce da ke nuni da cewa a yanzu gwamnati ta kara matso da harkokin ciyar da al’ummarta gaba kusa da jama’a.
“Nan ba da dadewa ba gwamnati za ta nada mambobin majalisar sababbin masarautun domin kama aiki ka’in-da-na’in. Don haka ina horon sababbin sarakuna da su dage don ganin cewa sun samar wa jama’arsu ci gaba ta fannin ilimi da kiwon lafiya da noma da sauran fannonin rayuwa. Gwamnati a shirye take ta ba wadannan sababbin masarautu goyon baya domin ganin sun ciyar da al’ummarsu gaba,” inji Gwamna Ganduje. Wadansu ’yan asalin Jihar Kano da suka tofa albarkacin bakinsu game da kirkiro sababbin masarautun, sun shaida wa Aminiya irin yadda wannan al’amari ya zo musu.
Malam Yusuf Ibrahim Gyadi-Gyadi ya bayyana takaicinsa na raba Masarautar Kano gida biyar. Ya ce, “A gaskiya ban yi farin ciki da faruwar wannan al’amari ba, domin ba zai kawo mana ci gaba ba. Hasali ma rabe-raben kai zai haifar a tsakanin al’ummar Jihar Kano. Duk da cewa ana ba da misali da Jihar Jigawa wadda ke da masarautu biyar, a ganina su ma suna fama da matsalar rabe-raben kai a tsakanin al’ummarsu. Kuma idan aka yi la’akari da yadda lamarin ya faro za a tarar akwai siyasa a ciki, wanda haka ke nuni da cewa lamari ne na ramuwar gayya kawai.” Shi kuwa
Iliyasu Abdullahi ya koka ne ainun kan kirkiro sababbin masarautun, yana mai cewa a gaskiya bai kamata a kirkiro masarautun ba, domin babu wani dalili kwakkwara kan hakan ya kamata.
“Kamata ya yi a ce jama’ar yankunan da abin ya shafa ne suka nemi a yi musu masarautu ba wani ayarin lauyoyi ba kamar yadda abin ya faru. Wannan na nuni da cewa gwmanati ce ke son kirkiro masarautun ba al’ummar da abin ya shafa ba. Abin tsoroshi ne, zai iya yiwuwa a rushe masarautu duk lokacin da aka samu sabuwar gwamnati nan gaba, wanda haka kan iya zama koma baya ga jihar da al’ummar da abin ya shafa.”