Uban gidansa ya sallame shi daga aiki ana dab da a yaye shi a kuma shi jari shi ma ya bude shagon sayar da kayan motoci, kamar yadda suka yi yarjejeniya.
Bayan rasa aikin da kuma jarin da yake sa ran za su sa shi ma ya zama hamshakin dilan kayan motoci, matashi Kingsley Ude ba shi da zabi face ya sake fara rayuwa sabuwa fil daga tushe. Amma ta ina zai faro, domin ba sana’ar da ya iya sai sayar da kayan motoci?
To amma yaya aka yi ya zama miloniya? Ku biyo Aminiya ku sha labari.
Bayan burinsa na zama dilan kayan motoci ya samu cikas, Mista Ude bai yi tantamar tsunduma harkar sayar da kayan abinci ba.
Kafin sana’ar busashshe da kuma gasashshen kifi da ta mayar da Mista Kingsley hamshakin dan kasuwa, ya fuskanci kalubale iri-iri.
Ude ya fara da karamin jarin N6,OOO a kasuwar kifi ta Kado da ke yankin Jabi na Babban Birnin Tarayya Abuja, amma yanzu ya zama hamshakin miloniya.
Ta yaya hakan ta faru?
“Lokacin da na fara kasuwanci teburi ne da ni a tsakiyar rana, nakan tambayi kaina, tsawon wane lokaci ne zan ci gaba da sayar da busashshe da kuma gasashshen kifi a leda kullin Naira 20 da Naira 50?
“Na damu matuka.
- Na ki karbar aikin gwamnati saboda sana’ar fim – Ali Nuhu
- Gwamnatin Tarayya za ta kirkiro ayyukan yi miliyan biyar
“Kafin na fara sana’ar kifin, ina da wani tsohon mai gida da ya ke shigo da kayan motoci inda muka yi yarjejeniyar shekara biyar za a sallame ni.
“Yarjejeniyar ita ce bayan shekaru biyar din zai ba ni jarin kai na da ni ma zan fara harkar kayan motocin.
‘Iftila’i ya fada min’
“Kwatsam sai wani ifti’la’i ya saukar min.
“Shekara daya kafin lokacin yayen nawa ya yi kawai sai maigidan ya sallami yaransa mutum 17, ciki harda ni.
“Ya yi hakan ne sakamakon wata damfara da aka yi masa yayin wata cinikayya a kasar Japan.
“Duk lissafina ya rikice. Yanzu dole in fara komai daga farko kenan.
‘Duk da haka ban karaya ba’
“A hakan dai ban karaya ba, sai na sayi babur na fara sana’ar acaba daga ‘yan kudaden da na iya tarawa.
“A sana’ar ce na tara ribar N6,000 da na yi amfani da ita a matsayin jarin fara sana’ar tawa a shekarar 1999.
“Na sayi injin sarrafa hatsi a kan N1,200, sai buhun garin kwaki a kan N300, buhun doguwar shinkafa a kan N1,700, buhun gajeruwar shinkafa akan N1,700, na kuma sami teburin katako inda na fara awon kayan kwano-kwano.
Daga sayar da kayayyakin a kan tebur cikin tsakiyar rana a kasuwar kifi ta Kado, daga baya Ude ya samu wani wurin a inuwa kafin likkafa ta kara gaba ya sami shago lokacin da aka gina kasuwar.
“A lokaci kudi na da daraja, na samu na iya tsayawa da kafata, amma in yanzu ne wannan jarin ba abin da zai yi maka.
‘Lokacin ana canzar da Dala ne akan Naira 67. Ko a lokacin da abubuwa suka ta’azzara ma na yi ta maza na ci gaba da harka.
‘Akwai riba a sana’ar sosai’
“Sana’ar busashshe da kuma gasashshen kifi tana da matukar riba ta yadda kowane bangare na kifin ake yi masa filla-filla kuma a sayar da shi daban.
“Muna sayar da buhun kan busashshen kifi a kan N85,000, yayin da ake sayar da kifi mara kaya a kan N18,500 kan kowane kilogriram biyu, sai kuma buhun zallar tsokar kifin ake sayar da shi a kan Naira dubu dari hudu da tamanin.
‘Sana’ar ta yi min komai a rayuwa’
“Da wannan sana’ar, na sami damar daukar nauyin karatun dukkan kannena, kai akwai wanda na tura kasar Jamus ma ya yi karatunsa a can.
“Da ita ne kuma na sami nasarar sayen mota, na gina gida kuma na yi aure.
“Yanzu sakamakon wannan sana’ar ina iya kula da ‘ya’yana yadda ya kamata. To me kuma nake bukata a rayuwa? Sai hamdala gaskiya”.
Da yake bayanin yadda annobar coronavirus ta shafi kasuwancin nasa, Mista Ude ya ce ta shafi farashin saye da kuma na sayarwa duk sun yi tashin gwauron zabi.
“Yawancin kwastomominmu yanzu ba sa iya sayen kaya.
“Kasancewar na dade a wannan harkar, na fahimci kwastomomina na hakika kuma nakan ba su bashi idan na fahimci ba su da kudi.
“Kan busashshen kifi guda daya da ake sayarwa N500 a da yanzu ya koma N800.
“Kazalika, buhun busashshen da a baya ake sayarwa N65,000 yanzu ya koma N65,000.
“Buhun kan kifi da ake sayar da shi N62,000 yanzu ya koma N85,000.
“Lokacin da na fara sana’ar, buhun busashshen kifi ba ya wuce N700 zuwa N1,000.
“Lokacin mutane ba ma ruwansu da kai ko kayar kifin, amma yanzu wadannan sassan da ake gudunsu a da yanzu mutane rububinsu suke yi saboda neman sauki.
Yadda annobar coronavirus ta shafi sana’ar
Makonni biyu da suka shude, Mista Ude ya sayo tare da biyan kudin busashshen kifi buhu biyu daga garin Aba, amma amma ba su karaso Abuja ba.
Ya ta’allaka yawan jinkirin da ake samu wajen isoawar kaya da dokar takaita zirga-zirga tsakanin jihohi, yana mai cewa da zarar aka cire dokar baki daya, ‘yan kasuwa za su rage yawan kudaden da ake tatsa daga hannunsu a manyan hanyoyi wanda hakan kuma zai saukar da farashin kayayyaki.
Ya kuma ce hakan zai saukaka wa masu sayen kaya.
Kazalika, wata ‘yar kasuwa da ta koyi harkar sayar da kayan abincin daga mahaifiyarta tun shekara ta 2007 mai suna Nancy Chukwumba ta ce mahaifiyarta ta fara harkar ne sama da shekaru 25 da suka wuce.
Misis Janet Chukumba, mahaifiyar Nancy, ta fara sana’ar ne da sayar da fufu, da aka fi sani da akpu da kuma garin rogo a bayan makarantar sakandare ta Gwarimpa.
Ta ce lokacin girbin amfanin gona (kaka), sukan sarrafa rogon su mayar da shi fufun.
Kasuwancin Nancy ya ci gaba da bunkasa tsawon shekaru ta yadda yanzu haka ta kai ga ta mallaki wuri mai matukar muhimmanci a kasuwar.
“Mukan sayi ganyen Uziza da na daga kasashen ‘Inyamjurai, sai kuma kwakwar manja daga kasashen Kudu maso-Kudu.
“Kafin dokar kulle, a kan sayar da buhun garin rogo N9,OOO, amma yanzu ya kai N19,000”, inji Nancy.