Aƙalla matasa 136 ne, suka baje-kolin fikirarsu a fannin ƙirƙire-ƙirƙiren na’urori daban-daban masu amfani ga rayuwar al’umma a Jihar Kano.
Yayin da matasa a faɗin duniya ke murnar wannan rana da aka yi wa take da ‘WORLD YOUTH SKILL DAY’ matasa a Jihar Kano, ma ba a bar su a baya ba.
- Kotu ta tabbatar da nadin Sanusi II a matsayin Sarkin Kano
- Hauhawar farashin kayayyaki ya ƙaru zuwa kashi 34.19
Matasan sun fito domin nuna baiwarsu da ƙwarewarsu a fannin ƙirƙirar na’urorin zamani da sarrafa kayayyaki na cikin gida domin amfanin al’umma.
Taron bajekolin na bana ya gudana ne a Cibiyar Aliko Dangote Skills & Acquisition Centre.
Ko’odinatan cibiyar, Alkasim Husaini Wudil, ya ce matasa 136 ne suka ciri tuta ta hanyar ƙirƙirar manyan na’urori daban-daban da za su taimaki al’umma a fannin noma, ilimi, kasuwanci da sauransu.
Daga cikin matasan masu fikira da suka halarci taron na bana, akwai Khalifa Aminu, matashin da ya ƙirƙiro gilashi da yake taimaka wa makafi wajen yi musu jagora wanda ya ce a yanzu haka ya sake ƙirƙirar na’urar da ta ke sarrafa kanta wajen fesa ruwa a gona.
Kazalika, akwai Haruna Badamasi, matashin da ya ƙirƙiro jirgi mara matuƙi, wanda a cewarsa yana taimaka wa manoma wajen feshin magani.
Har wa yau, jirgin yana da tanki wanda yake iya ɗaukar lita biyu na ruwan maganin ƙwari domin feshin gona.
Da yake jawabi a wajen taron, Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, wanda ya samu rakiyar Ministan Matasa na Najeriya, Sunday Akin Dare, ya ce gwamnati za ta ci gaba da tallafawa cibiyar da sauran makarantu masu koyar da ƙere-ƙere mallakin jihar, domin daƙile rashin aikin yi a tsakanin matasa.
Yusuf, ya ce muhimmancin wannan rana ne, ya sa gwamnatin jihar ta amince wa cibiyar shirya wannan taro domin bai wa matasa damar bayyana fikirarsu.
Ga hotunan yadda bikin ya wakana: