Garin Maiduguri, hedikwatar Jihar Borno, ya samun ruwan saman farko a daminar wannan shekara, inda aka shafe sama da awa guda na maka ruwa kamar da bakin kwarya.
Ruwan farkon ya zo ne da iska mai karfin gaske, inda aka fara ruwan tun bayan karfe uku na a rana, lamarin da ya yi sanadiyyar asarar dukiyoyi.
- Yadda matasa 29 suka rasu a nutsewar jirgin ruwa a Sakkwato
- Hadarin mota ya kashe malaman da’awa 6 a Kano
Ruwan da iskar sun yi sanadiyyar rugujewar wasu gidajen kasa baya ga asarar dukiyoyi ta miliyoyin Naira a garin na Maiduguri, inda a halin yanzu wasu wadanda abin ya shafa sun rasa muhallansu.
A zagajen da Aminiya ta yi a garin bayan daukewar ruwan, wakilinmu ya ga yadda iska ta kware rufin gidaje da dama tare da kayar da bishiyoyi a garin na Maiduguri.
Wakilinmu ya ruwaito cewa lamarin ya tilasta wa mutanen da abin ya shafa a unguwanni ke ta kokarin kwashe kayansu da baraguzan gine-ginen da suka rushe da kuma magudanan ruwa da suka cika makil.
Mun yi kokarin jin ta bakin Hukumar Agajin Gaggawa ta Jihar Borno, (SEMA) amma abin ya ci tura.
Amma wani jimi’in hukumar da ya bukaci a sakaya sunansa ya ce jami’an hukumar sun fara aikin tantance irin barnar da abin ya haifar domin daukar mataki na gaba.