✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda rungumar kaddarar Ahmed Lawan ta kawo karshen zamansa a majalisa na shekara 24

Tun da aka dawo Dimokuradiyya a 1999 ake damawa da shi a Majalisar Tarayya

Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Ahmed Lawan, na daya daga cikin ’yan Majisar Tarayya mafi dadewa a majalisar, inda ya shafe kimanin shekara 24 ana damawa da shi.

Lawan ya shiga Majalisar ne tun bayan komawar Najeriya mulkin dimokuradiyya a 1999, wato Jamhuriya ta hudu.

Ya zuwa karewar wa’adin Majalisa ta tara a watan Yunin 2023, zai zamana Lawan ya cika shekara 24 da shiga majalisar kasa.

Sai dai kuma, ga dukkan alamu zaman Lawan a Majalisar ya zo karshe bayan da ya rasa damar shiga takarar da zai nemi ci gaba da zama a cikinta a jam’iyyarsa ta APC.

Lawan ya rasa damar takarar Sanatan Yobe ta Arewa ne biyo bayan nasarar da Bashir Machina ya samu a kansa, kama daga lokacin zaben fid-da gwani har zuwa shiga kotu.

Masomin rasa wannan dama ga Lawan ya faro ne daga lokacin da ya shiga zaben fid-da gwani na takarar Shugaban Kasa karkashin jam’iyyarsu ta APC, amma bai kai bantensa ba.

Duk da cewa Lawan bai shiga zaben fid-da gwani na neman Sanata ba, amma APC ta aika wa hukumar zabe ta INEC sunansa a matsayin dan takararta a Yobe ta Arewa, lamarin da hukumar ta ki amincewa da shi.

A hannu guda, Machina wanda duniya ta shaida shi ne ya lashe zaben fid-da gwanin, ya yi tsayin daka tare da cewa ba zai janye takararsa ga kowa ba, saboda shi ma yana da bukatar ba da gudunmawarsa ga ci gaban yankinsu.

Lamarin da ya kai su ga shiga kotu wanda a ranar Laraba, wata Babbar Kotun Yobe ta yanke hukunci inda ta ba da umarnin INEC ta riki Machina a matsayin halastaccen dan takarar sanata a yankin nasu, daga bisani shi kuma Ahmed Lawan din ya ce ya rungumi kaddara, ba zai daukaka kara ba.