A ranar Litinin da ta gabata ce wata Kotun Shari’ar Musulunci da ke zamanta a Kano ta yanke wa tsohuwar jarumar Kannywood, Sadiya Haruna, wadda a yanzu take kasuwancin sayar da kayan mata da na karfin maza hukuncin daurin wata shida a gidan yari ba tare da zabin biyan tara ba.
An gurfanar da ita ne a gaban kotun bisa zargin bata sunan wani tsohon jarumin masana’antar Isa A. Isa.
- Za a fara biyan mata masu juna biyu N5,000 duk wata a Jigawa
- Amurka ta bukaci ’yan kasarta su gaggauta ficewa daga Ukraine
Alkalin kotun Mai Shari’a Muntari Garba Dandago ne ya yanke hukuncin, inda ya aike da Sadiyan gidan yari saboda samunta da bata sunan Isah.
Aminiya ta ruwaito a makon jiya cewa wani sabon rikici ya barke bayan an samu wani faifan bidiyo na Sadiya Haruna tana kuka, inda take cewa lallai tana neman agajin mutane domin rayuwarta na cikin hadari.
A cikin bidiyon, ta ce an kai mata hari a shagonta, inda ta yi zargin ana so ne a watsa mata ruwan guba na acid a fuskarta.
Ta kuma yi zargin an kama kaninta da zargin satar waya, inda ta ce kaninta ya fi karfin ya saci waya.
A cikin bidiyon, ta zargi wasu da ce marasa tsoron Allah da mace da na namiji. Sai dai ba a san ko su wa take ba.
Jim kadan kuma sai ga bidiyon Fati Slow, inda kai tsaye ta kira sunan Sadiya Haruna ta ce ba hari aka kai mata ba, ’yan sanda ne suka je kama ta, amma ta gudu.
A cewar Fati Slow, Teema Makamashi ta wuce da sanin Sadiya Haruna. Ana cikin hakan ne, sai Chizo Germany ya fitar da wani bidiyon, inda yake yin kira da a sanya baki a rikicin na Sadiya Haruna da Teema Makamshi.
A cewarsa, ya sha ya shirya tsakaninsu, amma kuma daga baya su ci gaba. A karshe ya yi kira ga mahukunta a Kannyood da masu fada a ji a Jihar Kano da sanya baki domin a samu maslaha.
Ya kara da cewa ya san duk abubuwan da suka kawo rigimar, amma shi ba zai dauki bangare ba, domin duk mutanensa ne, amma ya yi musu kashedin cewa idan ya fara bude magana fa akwai matsala.
Ana cikin haka ne sai aka samu labarin kotu ta yanke mata hukuncin daurin wata shida a gidan yari ba tare da zabin biyan tara ba.
Yadda rigimar ta samo asali
A shekarar 2019 ce aka fara rigimar bayan Sadiya Haruna ta fito ta yi kaca-kaca da Isah A. Isah bisa zarginsa da yin auren mutu’a da ita da sa mata cuta da zarginsa da luwadi da sauransu.
Sai dai ko a lokacin, Isah A. Isah ne ya fara fitowa ya saki wani bidiyo, inda a ciki yake neman afuwar mutane bisa wani kuskure da ya yi da bai ambata ba. Wannan bidiyon ne ya tunzura Sadiya, inda ta saki bidiyo, a ciki take cewa a lokacin, “Isah, ni Sadiya Haruna na ce maka kai dan luwadi ne, na ce maka kai mutumin banza ne.”
A wani bangare na bidiyon kuma cewa ta yi, “Isah so nake yi ka fito ka ce kai ba dan luwadi ba ne, so nake ka fito ka ce ba mu yi auren mutu’a ba, auren wata uku auren sha’awa.”
Daga baya Sadiya Haruna ta bayyana a wani bidiyon cewa abin da ya hada su fada shi ne ya mata ciki ne, sannan ya sa ta ta zubar wanda hakan ya sa ta kamu da ciwo.
Sannan ta ce ya sanya Sadiya Haruna Isah A. Isah mata ciwon sanyi wato infection mai zafi. Sai dai tun a lokacin Isah A. Isah ya fito ya karyata batun, inda ya ce shi karya ta yi masa bai aure ta ba.
Sai dai ya ce lallai matarsa ta bata masa rai, inda suka hada baki da Sadiya a kan ta ce ya aure ta, kuma hakan suka yi. Ya kara da cewa shi taimakonta ya yi bayan ta zo masa da cewa ’yan fim sun cuce ta.
Tun a wancan lokacin Isah A. Isah ya kai karar Sadiya Haruna wajen ’yan sanda, inda a watan Oktoba na shekarar 2019 ’yan sanda suka kama ta A ranar 16 ga watan na Oktoba na shekarar 2019, kotu ta saurari karar, inda bayan Sadiya ta karyata tuhumar da ake mata, kotu da daga shara’ar, sannan ta yi umarni da a tsare Sadiya Haruna.
Sai dai tun nan ba a sake jin duriyar shara’ar ba, sai wannan lokaci.
A wannan lokacin kuma, an zaci rikicinta da Teema Makamashi ne, sai aka ji ashe tun wancan rigimar ce da Isah A. Isah.
Za mu tanadi garin kwaki don ziyartar gidan yari – Teema Makamashi
A wani dan takaiccen bidiyo da Aminiya ta gani, Teema Makamashi ta fito tana murnar daure Sadiya Haruna, inda a ciki take cewa an daure Sadiya a gidan yari, kuma za su tanadi garin kwaki da burodi da ruwan leda domin ziyartar gidan yari domin a cewarta su ba sa gaba.
Ina godiya ga Allah-Isah A. Isah Shi ma wanda ya kai karar Sadiya Haruna din, Isah A. Isah ya bayyana godiyarsa ga Allah kan wanna hukunci da kotu ta yanke, inda ya ce, “bayan kwashe shekara biyu da wata uku da wasu kwanaki muna shara’a da yarinyar nan da ta fito kafafen sadarwa ta ci mutuncina, yau kotu ta wanke ni, sannan kotu ta daure ta. Ina godiya ga Allah. Da ma na dade ina fada wa Allah. Allah Ya yi min sakayya Allah Ya tabbatar min da nasarata,” inji shi a wani bidiyon da ya saka.
Rigimarta da Alassan Kwalle
A wata rigimar daban, Sadiya Haruna ta taba zargin Shugaban Kungiyar Jaruman Kannywood, Alhassan Kwalle da cewa ya neme ta da lalata a Maiduguri.
A lokacin shi ma Alhassan Kwalle ya kai ta kara wajen ’yan sanda, inda aka kamata kafin aka ba da belinta.
Yadda Sadiya Haruna ta koma wakokin bege
Ana cikin haka, sai kwatsam a shekarar 2020, aka wayi-gari Sadiya Haruna ta canja sunanta a Instagram, inda ta koma Sayyada Sadiya Haruna, sannan ta fara wakokin begen Manzon Allah.
Daga cikin wakokin da ta yi akwai bidiyon da ta yi na wakar ‘Ita kadai hujja ce’ da sauransu.
Batsa a kafofin sadarwa Duk da cewa Sadiya Haruna ta fara fim ne, amma ta zo ta yi kaurin suna ne wajen tallata kayan mata da na karfin maza a kafofin sadarwa, inda take fitowa fili tana bayani ba tare da boye komai ba.
A wani bidiyo, ta fito tana bayyana yanayin gaban namiji ta hanyar amfani da roba da bayanin saduwa da sauransu.
Hukuncin komawa makarantar Islamiyya
Bisa dalilin fitowa tana bayanai irin wannan ne, Hukumar Hisbah ta kamata tare da kai kararta, inda a dalilin haka aka gurfanar da ita da a wata kotu da ke zaman a Sharada na Jihar Kano bisa tuhumar amfani da kafafen sada zumunta da YouTube wajen yada hotuna da bidiyon batsa.
A nan Alkalin kotun, Mai Shari’a Ali Jibril Danzaki, ya yanke mata hukuncin shiga makarantar Islamiyya ta Darul Hadith da ke Tudun Yola, a Kano na tsawon wata shida a matsayin hukuncin laifin da ta aikata.