✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Yadda rikicin Boko Haram ya lakume rayukan yara 300,000 a Arewa maso Gabas

“Akwai wasu da dama da har yanzu ba a san inda suke ba, wasu an sace su."

Sama da yara 300,000 ne suka rasa rayukansu a cikin shekaru 12 da suka gabata sanadiyyar ayyukan ta’addancin Boko Haram a Arewa maso Gabas, kamar yadda wani sabon rahoton Asusun Kula da Kananan Yara na Majalisar Dinkin Duniya (UNICEF) ya nuna.

Hakan na zuwa ne a daidai lokacin da Rundunar Sojojin Najeriya ta ce kungiyar ISWAP ta fara dibar sabbin matasa marasa aikin yi domin su shiga cikinta ta ci gaba da ta’asa.

Alkaluman na UNICEF na kwanan nan sun kuma ce sama da mutum miliyan daya ne rikicin ya raba da muhallansu a cikin wannan lokacin.

Rahoton ya kuma ce akalla yara 5,129 wadanda basa zuwa makaranta ne yanzu haka suke fama da matsalolin rashin lafiya sakamakon rikicin a Arewacin Najeriya.

Da wakilinmu ya bukaci karin bayani a kan musabbabin mutuwar yaran 300,000, jami’in hulda da jama’a na UNICEF a Maiduguri, ya ce alkaluman jimlar wadanda suka mutu ne sanadiyyar hari na kai tsaye da ma wanda ba na kai tsaye ba.

Ya ce, “Yaran sun mutu ne yayin musayar wuta ko fashewar bama-bamai ko an yi amfani da su a matsayin ’yan kunar bakin wake ko kuma yunwa ce ta kashe su da ma sauran dalilai.”

Shi ma wani tsohon soja, Salihu Bakari ya ce sam alkaluman na UNICEF ba su zo masa da ba-zata ba.

“Kawai dai mun fara fuskantar zahirin abubuwan da ke faruwa ne a baya saboda yawan hare-haren da ake kai wa. Ba mu cika mayar da hankali wajen bayar da agaji ko bibiyar halin da yara suke shiga ba.

“Na tabbatar a cikin watanni masu zuwa za a fitar da karin wasu alkaluman, amma abu mafi muhimmanci shi ne a gano yadda za a kawo karshen matsalar.

“Akwai wasu da dama da har yanzu ba a san inda suke ba, wasu an sace su, wasu na hannun ’yan ta’adda, suna nan sun horar da su don su zama mayaka.

“Saboda haka, yayin da muke ci gaba da nuna alhini da kisan wadannan yaran, ya zama wajibi a tashi tsaye wajen ceto wadanda suke hannun ’yan ta’adda don a sauya rayuwarsu,” inji Salihu.

Sai dai Babban Jami’in hukumar UNICEF a Najeriya, Peter Hawkins ya ce dole dukkan masu ruwa da tsaki su taka rawa wajen ganin an kawo karshen kai hari kan kananan yara da gaggawa.