Wani fasto tare da wasu matasa biyu ’yan uwan juna sun riga mu gidan gaskiya bayan da suka afka cikin rijiya a yankin Owode-Ede da ke Jihar Osun.
Iftila’in ya auku ne bayan daya daga cikin matasan da suke aikin birkila ya yi kokarin ciro gugarsu da ta fada cikin rijiyar.
- Matar da ke kai wa ’yan bindigar Zamfara makamai ta shiga hannu
- 2023: ‘Hausawan Ebonyi’ sun goyi bayan dan takarar Gwamnan PDP
Kamfanin Dillancin Labarai na Najeiya (NAN) ya tattaro cewa daya daga cikin matasan da lamarin ya shafa ya fara yukurin ciro gugar da ta fada cikin rijiyar, inda shi ma ya fada cikin rijiyar.
Faston da dayan matashin sun bi baya ne bayan da suka yi kokarin ceto na farkon da ya fada.
A cewar mai magana da yawun Hukumar Kwanan-kwana ta jihar, Adekunle Ibrahim: “Lamarin ya faru ne a kauyen Alaro Onigbin a yankin Owode Ede, cikin Karamar Hukumar Ede ta Arewa.
“Wani Fasto Adebayo Oluwasina, ne ya bai wa matasan, Lateef Adediran da Waliu Adediran, aikin gina katangar makarantarsa.
“Yayin da suke bakin aiki, sai wanda ke debo musu ruwan aiki a rijiyar gugarsa ta fada cikin rijiyar inda ya yi kokarin ciro ta.
“Ganin dan uwansa ya fada rijiya ya makale, hakan ya sa yayan shiga rijiyar domin ceto shi, amma suka makale tare,” in ji shi.
Ya ci gaba da cewa, ganin abin da ya faru ya sa shi ma fasto ya shiga rijiyar don kai musu dauki, inda shi ma ya makale.
“A daidai wannan gabar aka sanar da mu abin ke faruwa,” in ji Ibrahim.
Jami’in ya ce an samu ciro gawarwakin tare da gudunmawar jami’ansu da na ’yan sanda da mazauna yankin.
Ya ce an tabbatar da mutuwarsu ne bayan da aka kwashe su zuwa asibiti, daga bisani aka mika su ga ’yan uwansu.
(NAN)