✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda rijiya ta ci magininta da dansa da mutum biyu a Sakkwato

Wata rijiya ta ci mutum hudu ciki har da mai shirin zuwa hidimar kasa (NYSC), bayan sun shiga cikin rijiyar don ceto wanda ya shiga…

Wata rijiya ta ci mutum hudu ciki har da mai shirin zuwa hidimar kasa (NYSC), bayan sun shiga cikin rijiyar don ceto wanda ya shiga don yashe ta a Unguwar Baiti da ke Karamar Hukumar Yabo a  Jihar Sakkwato.

Wanda ya gina rijiyar kuma sanannen maginin rijiyoyi a yankin Malam Muhammad Umar Mai Zuma wanda aka ce ya shafe fiye da shekara 40 yana ginar rijiya a yankunan  Sakkwato, ya gamu da ajalinsa ne ta hanyar wannan sana’a da yake yi a ranar Lahadin da ta gabata inda aka kira shi don yashe wata rijiya da ruwanta ya gurbace.

Kuma bayan da ya shiga rijiyar aka daina jin motsinsa ne sai aka sanar da dansa Abubakar da suka zo da wani mai suna Yahaya Sani da Zaharadden Dodo matashin da ya shirya don tafiya hidimar kasa (NYSC) a Jihar Osun suka rika shiga bi da bi amma duk suka rasu.

Aminiya ta ziyarci karamar hukumar kuma ta zanta da mai rijiyar mai suna Aliyu Shekare Yabo wanda aka fi sani da Miloniya, inda ya ce:  “Ni ne mai wannan rijiyar da wannan lamarin ya faru. Ruwan rijiyar ne ya lalace yana wari kimanin kwanaki biyar. Sai na yanke shawarar yashe rijiyar, na nemi Shugaban Karamar Hukuma ya ba ni motar da za ta kwarfe ruwan sai na sanya a duba rijiyar. Marigayi Mai Zuma ya zo amma kafin nan mota ta kwashe ruwan gwargwardon abin da take iyawa, cikin minti 30 sai ya shiga domin duba ko wani abu ne ya fada ko kuma yashewa  take bukata.”

Ya ce,  “Kafin ya shiga sai  na shiga cikin gida don cin abinci.  Ina ciki ne sai yarinyata ta sheko da gudu ta ce mai ginar rijiya ya shiga ciki, amma ba a ji duriyarsa ba.”

Ya ci gaba da cewa “Ban tsaya ba na tafi inda dansa ke aiki na sanar da shi suka taho tare da wadanda yake aiki da su, wani mai babur ya dauko shi don ya yi sauri ya riga mu zuwa. To katin wayata ya kare sai na tsaya a wani shago na saya, nan ne wadansu suka tare ni suka hana ni zuwa gida saboda abin da yake faruwa, har sai komai ya lafa.”

Ya ce yanzu ya rufe rijiyar yana jiran shawarar da mahaifansa za su yanke kan ya ci gaba da amfani da ita ko akasin haka.  Ya ce rijiyar shekararta daya da wata biyu da ginawa, kuma Mai Zuma ne ya gina ta da kansa.

Wakilinmu ya zanta da  Amiru Sani kanen daya daga cikin mamatan da aka yi komai a gabansa ya ce: “Bayan an yi duk mai yiwuwa wajen ganin an kwarfe ruwan rijiyar da ke wari abin ya faskara sai aka kira Mai Zuma. A lokacin da ya shiga rijiyar sai aka ji shiru daga nan ne aka sanar da dansa, inda shi kuma ya tafi tare da wadansu mutum biyu da suke aiki tare.  Daga nan dukkansu su ukun suka shiga ciki tun daga nan ba a sake jin duriyarsu ba.”

“Abin ya faru tun karfe 9:30 na safe amma ba a fitar da su ba sai karfe 1:30 na rana, sai da aka kira Dan Sarkin Ruwan Argungu sannan aka ciro gawarwakinsu,” inji shi.

Da ya juya kan masu zargin hayakin inji ne ya kashe su  a cikin rijiyar, sai ya ce lallai ya ga injin da Mai Zuma ya buge har sai da ya lankwashe amma a lokacin injin ba ya fitar da hayaki, al’amarin da ya sa ake zargin akwai aljannu a ciki.

Zuwa hada wannan labari an rufe rijiyar ana jiran matakin da hukuma za ta dauka.

Wakilinmu bai samu damar tuntubar bangaren ’yan sanda game da faruwar wannan al’amari ba.