✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Yadda rasuwar Sarauniyar Ingila ta kawo wa ’yan kasuwa ciniki

’Yan kasuwa a Buckingham sun ce jimamin rasuwar Sarauniya Elizabeth II ta kawo musu karin ciniki.

’Yan kasuwa a Buckingham, yankin Fadar Masarautar Ingila, sun ce rasuwar Sarauniya Elizabeth II, ta kawo musu karin ciniki.

Masu shaguna da otel-otel a Buckingham da ke birnin London sun ce cikinsu ya karu sosai tun bayan rasuwar sarauniyar har zuwa lokacin da aka kaddama da babban danta, a matsayin sabon sarki —Charles III.

Sun ce karin cinikin ya shafi bangaren abinci zuwa masu neman masauki da masu sayen furanni da saurnan kayan kyaututtuka da ke dauke da hoton marigayiyar.

Manajar kamfanin Cool Britannia, masu kayan kyaututtukan alfarma da ke Buckingham, Patricia Hajali, ta shaida wa kafar yada labarai ta DW cewa ana rububin sayen “Duk abin da ke dauke da hoton Sarauniya,” musamman rigunan T-Shirt da kananan kofuna da zobuna da maballai da sauransu

Shagon furannin ta'aziyya
Shagon furannin alfarma na Pulbrook & Gould na fatan samun karin ciniki a lokacin jana’izar Sarauniya Elizabeth II. (Hoto: DW)

Jimamin rasuwar Sarauniya

Sai dai duk da haka, a lokacin kaddamar da Charles III, yanayin yankin da ke makwabtaka da Fadar Buckingham ya kasance babu annuari sosai, idan aka kwatanta da  yadda aka saba ganin mutane cikin murna a lokacin rayuwar mahaifiyarsa Sarauniya Elizabeth II.

Manajar kamfanin Cool Britannia, Patricia Hajali, ta ce juyayin mutuwar sarauniyar zai sake dawowa a zuwa ranar  Litinin 19 ga watan Satumba da muke ciki da za a yi jana’izarta.

“Amma ina ganin juyayin ya fara raguwa zukatan mutane, kamar sauran lokuta, amma duk da haka mun dakatar da sanya kade-kade saboda girmamawa.”

Furannin ta’aziyya

Shagon Pulbrook & Gold masu sayar da furannin ta’aziyya na alfarma da na sarauta a Layin Fadar Buckingham sun ce su ma cinikinsu ya karu sosai.

Manajan wurin, Erik Karlsen, ya ce mutane na yin tururuwa zuwa sayen furannin ta’aziyya kuma yawanci sun fi  sayen na lambu domin bankwana da sarauniya.

Erik Karlsen mai shekara 63, ya ce yawanci suna yin haka ne, “Saboda yadda ta sadaukar da kanta ga yankunan karkarar Ingila da kuma shakuwarta da lambu da furanni.”

Tsadar kaya

Sai dai kuma kwastomomi na kokawa bisa yadda suka ce ’yan kasuwar ke tatsar masu sayen kayan kyaututtuka.

Wani dattijo mai shekara 54 da ya je London domin ta’aziyya tare da ’yarsa budurwa, sun koka bisa tsananin tsadar furannin Pulbrook & Gould.

Sun bayyana cewa akwai alamar tatsar kwastomomi a yadda ake sayar da fure a farashin €11.55.

Amma manajan shagon, Mista Karlsen ya ce yana fata gidan sarautar zai biya shi kamasho gabanin jana’izar sarauniyar.

A cewarsa, Pulbrook & Gould ya shirya bukukuwan aure da sauran shagulgula da dama a tsaon shekaru.

Patricia Hajali,
Patricia Hajali, Manajar Cool Britannia ta ce tana fata kayansu za su kayatar. (Hoto: DW)

Ya kuma kara dac cewa, shi kansa ya fito ne daga tsatson Jamusawa, kuma cikakken sunansa Erik Karlsen von Wettin, don haka  yana tunanin idan aka bincika za a iya samu yana dangatakada Sarauniya Elizabeth.

Karuwar neman masauki

Shi ma otel din The Rubens da ke kan Layin Fadar Buckingham, ya samu karin kwastomomi masu kama masauki.

Sun ce sun fi samun cinikin ne musamman ranar Juma’a, washegarin rasuwar Sarauniya kuma jajibirin nada Sarki Charles III.

Joan Goncalves mai shekara 63 dan asalin kasar Portugal ya ce, “Kusan kowa yanzu London yake tafiya,” kamar yadda ya shaida wa kafar yada labarai ta DW.

Three porters outside a hotel entrance

Hasashen karin ciniki

Kazalika, masu otel-otel na kyautata zaton baki za su kama dakunansu gaba daya a lokacin taron jana’izar sarauniyar da za a yi ranar Litinin, 19 ga watan Satumba da muke ciki.

A Cool Britannia kuma, Hajali ya ce sun yi odar kayan kyaututtuka masu dauke da hotunan Sarki Charles III, wadanda zuwa ranar Laraba za su iso shagon.

Sai dai ya ce duk da haka suna ganin za su fi samun cinikin abubuwa masu dauke da hotunan Saruaniya Elizabeth II.

Hajali ta bayyana cewa kawo yanzu, ba su samu mutane sosai ba da ke son sayen hotuna ko kayayyaki masu dauke da hotun sabon sarkin.

Hajali ta ce tana fata za zu samun cinikin abubuwa masu hoton Charles’ a lokacin mulkinsa, amma ba za ta iya cewa ko cinikin zai kai na masu dauke da hotunan mahaifiyarsa ba?

“Ba na tunanin haka, saboda ita ta shafe tsawon shekaru a matsayin sarauniyarmu,” in ji ta.