✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Yadda rashin wutar lantarki ke ruguza kasuwanci a Najeriya

Hajiya Habiba Balogun ta bayyana cewa rashin wutar lantarki ya janyo kasuwancinta ya tsaya cak.

A cikin ’yan watannin nan ana fama da matsalar rashin man fetur da gas, matsalar ta yi naso a kan rashin wutar lantarki, inda a jihohi da dama ke fama da rashin wutar lantarki.

Aminiya ta tuntubi bangarorin ’yan kasuwa da masana kan yadda rashin wutar lantarkin yake ruguza al’amuran kasuwanci da na yau da kullum.

Jihar Kano

Harkokin kasuwanci a Jihar Kano suna ci gaba da samun koma-baya saboda rashin isasshiyar wutar lantarki da hakan ya janyo karin tsadar kayayyaki, a gefe guda kuma ya haifar da karancin riba.

Hakan ya janyo mafi yawan ’yan kasuwa da kamfanoni suka dan yi gyaregyare wajen gudanar da ayyukansu domin neman mafita game da halin da ake ciki.

Misali Gidan Rediyon Jalla da ke Kano ya bayar da sanarwar canza lokacin aikinsa inda aka mayar da shi daga karfe 1:00 na rana zuwa abin da ya sawwaka.

Wani ma’aikaci a gidan rediyon ya shaida wa Aminiya cewa lokacin da aka shiga matsalar wutar lantarki hakan ya tilasta wa gidan rediyon amfani da man dizal.

Ya ce bayan an fara amfani da dizal ne shi kuma farashinsa ya yi tashin gwaron zabo ya karu da kusan kashi 200.

Ya ce hakan ya tilasta gidan rediyon daukar wancan mataki duba da cewa ba za su iya ci gaba da gudanar da gidan rediyon ta amfani da man dizal ba.

A lissafin da suka yi sun gano cewa asara kawai suke yi.

Wani tela da Aminiya ta zanta da shi ya ce rashin wutar lantarki ya janyo masa koma baya a ayyukansa domin akwai kekunansa da sai da wutar lantarki suke aiki wanda kuma “A yau ga shi man fetur ba ya samuwa ballantana mu yi amfani da shi.

“Hakan ya tilasta na ajiye aikin gaba daya saboda idan na sayi man fetur na yi aiki da shi ba zan fita daga kudin aikin da za a biya ni ba.

“Idan kuma na kara kudi a kan kudin dinkin da aka saba biya na tabbas ba za mu daidaita da abokan huldana ba,” inji shi.

Ya ce a yanzu haka lamarin ya janyo cushewar aiki a wurinsa inda yake hangen lamarin zai shafi aikinsa na Sallah.

Ya ce “Abin da yake damuna shi ne aiki zai cunkushe min saboda baya ga dinkunan da ke gabana a yanzu kuma mutane har sun fara kawo dinkunan Sallah.

“Idan ba Allah ne Ya sa aka samu wutar lantarkin nan ta daidaita ba, to babu shakka akwai matsala.”

Shi ma wani kamfanin ruwan leda na Ahsan Pure ya ce rashin wutar lantarki ya janyo ya dakatar da ayyukansa na wani lokaci.

Wata majiya da ta nemi a boye sunanta a kamfanin ruwan ta shaida wa Aminiya cewa shugaban kamfanin ya shaida wa ma’ikatansa cewa ba za iya ci gaba da yin aiki ba saboda ba ya samun riba a kan abin da yake yi a kullum.

“Shugaban ya shaida mana cewa saboda dizal ya yi tsada idan har suka yi aiki da shi ba su kirga riba sai faduwa. Kin san kuma kasuwanci don riba ake yi,”inji shi.

Ya ce a yanzu haka saboda tsayawar kamfanin ya janyo ma’aikatan kamfanin sun zama masu zaman kashe wando.

Majiyarmu ta kara da cewa ko da a ce kamfanin zai dawo da aikinsa to dole sai idan an samu gyaruwar wutar lantarki. Wata da ke gudanar da sana’ar gyaran gashi Hajiya Habiba Balogun ta bayyana cewa rashin wutar lantarki ya janyo kasuwancinta ya tsaya cak.

“Duba da rashin wutar lanatarki da kuma wuyar man fetur za ki ga aikinmu ba ya tafiya yadda ya kamata. Idan mun samu man fetur mu yi aiki idan ba mu samu ba, sai dai mu zauna mu yi hira a shago,” inji ta.

Ta ce a yanzu sun fi mayar da hankali wajen yin kitso da kunshi saboda halin da suke ciki. “Kin ga a da saboda muna aiki sosai ba mu tsayawa yin kitso ko kunshi saboda daukar lokaci da suke yi.

“Amma yanzu da aikin gyaran gashin ya zama sai a hankali, hakan ya sa muke neman mutanen da za mu yi wa kitso. Kin san kiran abokan hulda nake yi a waya idan suna bukatar kitso ko kunshi su zo a yi musu.

“Hakan yana taimaka mana sosai domin ba mu rasa dan abin da za mu sa a bakin salati har ma mu samu na biyan mota,” inji ta.

Jihar Legas

A Jihar Legas, kananan ’yan kasuwa na ci gaba da kokawa kan yadda matsalar rashin wutar lantarki da ake fama da ita a ’yan kwanakin nan ke sa su tafka asara.

Wadansu daga cikin ’yan kasuwar da Aminiya ta zanta da su sun ce matsalar ta yi kamari domin ta zo ne a lokacin da ake fama da matsalar man fetur da tsadar man dizal.

Muhammad Auwal matashi ne da ke sana’ar dinki a Legas ya shaida wa Aminiya cewa, “Yanzu lokaci ne na zafi, ba ma iya zama shago mu yi aiki idan babu wutar lantarki saboda zafi, kuma yawancin kekunan dinkin da muke amfani da su suna amfani da wutar lantarki ne ko janareta, rashin wutar da wahalar man fetir sun sa dole mu hakura da aikin, wanda hakan ke shafar tattalin arzikinmu, domin idan mun yi aikin babu fita sai asara.”

Alhaji Umar da ke da gidan sayar da abinci a Unguwar Oniwaya a Agege , Legas ya ce rashin wutar lantarki ya sa kasuwancinsu cikin garari, inda ya ce duk da karancin wutar, ma’aikata na ci gaba da neman kudin wutar lantarkin mai yawan gaske.

“Domin a yanzu haka a duk wata kudin da nake biya ya dara wanda nake biya a baya, amma babu wutar, kasuwancin da muke na bukatar mu kunna firiji domin adana kayan abinci, akwai bukatar mu kunna fankoki ko na’urar sanyaya daki domin idan masu cin abinci sun shigo kantin su samu natsuwa, don haka a yanzu kullum sai na sayi man fetur na Naira dubu biyar zuwa dubu shida,” inji shi.

Su ma coci-coci da masallatai kokawa suke yi da rashin wutar, a cewar Malam Shu’abu Sakataren Masallacin Lawal Atana, “Mutum ba zai gane mutane na cikin kuncin rashin wutar lantarki ba sai ya zo Sallar Asuba, Za ka ga mutane sun zo suna ta rige-rigen sa cajin waya.

Yanzu a masallacin muna sayen akalla man fetur na Naira duba hudu a rana domin dole mu kunna inji a lokacin Sallar Asuba har zuwa karfe bakwai na safe mu ja ruwan alwala, sannan a lokutan Sallar Azahar da La’asar a kunna akallla minti 30 kowace, sai kuma daga Sallar Magariba zuwa karfe 10 na dare kasancewar muna da ’yan makarantar dare da ke karatu bayan Sallar Isha’i,” inji shi.

Suleja

Wani mai masana’antar sarrafa roba a garin Suleja a Jihar Neja Malam Nura Muhammad ya ce masana’antun ’yan kasashen waje sun fi su samun wutar lantarki.

Ya ce hakan ya sa masana’antun sarrafa roba da suka kai 150 suka rufe a yayin da ragowar 50 kuma suka rage ma’aikatansu saboda asarar da ya ce suke tafkawa.

Ya ce kamafaninsa na biyan Naira dubu 700 duk wata na wutar lantarkin.

Ya ce duk korafi da suka gabatar a kungiyance ga kamfanin wutar lantarkin bai samu nasara ba, inda ya ce kamfanin ya sanar da su cewa tara kudi mai yawa shi ne babban burinsu. Wata majiya ta ce kamfunan sarrafa karafa biyu, wadanda daya yake yankin Sabon-Wuse, daya kuma a kusa da Jere, suna biyan Naira miliyan 600 kowanensu jimilla Naira biliyan daya da miliyan 200 a duk wata ga kamfanin wutar lantarkin.

Shi ko Alhaji Nuhu Muhammad wani mai kamfanin casar shinkafa a kauyen Tangan Wakili da ke Karamar Hukumar Tafa a Jihar Neja ya ce tuni ya daina amfani da wutar lantarkin ya koma amfani da injin wuta da ya kafa sakamakon karancin wutar da kuma tsadarta.

Ya ce ya kula cewa mitar wuta da kamfanin ya kafa masu kusan ba sa amfani da ita kasancewar ko an samu wutar ko ba a samu ba farashin a kullum sama yake kara yi ba tare da bambancewa ba.

“Haka kuma lamarin yake koda mun samu aiki ko ba mu samu ba,” inji Malam Nuhu