✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Yadda rashin tsaro ya sa ’yan Arewa dawowa daga rakiyar Buhari

'Tsige shi ya kamata, yanke kauna daga majalisa ce ta sa ake neman a sauka'

Ci gaba da watsuwar rashin tsaro a jihohin Arewa 19 ya sa mutanen Arewa da suka hada da dattawa da malaman jami’a da fitattun malamai da ’yan kasuwa da manoma da wadansu mutane dawowa daga rakiyar Shugaban Kasa Muhammadu Buhari.

Mutanen da suka fito daga mabambantan jam’iyyun siyasa da addinai da shugabannin shiyyoyi da a baya suke goyon bayan Shugaban Kasar, sun shaida wa Aminiya a tattaunawa ta musamman cewa Buhari ya yi matukar gazawa wajen cimma bukatu da fatar yankin, don haka suna bukatar ya yi murabus.

Kiraye-kirayen Shugaban Kasar ya sauka sun dada tasowa ne bayan kisan kiyashin da Boko Haram ta yi ga manoma a kauyen Zabarmari da ke Karamar Hukumar Jere a Jihar Borno a kwanakin baya.

Aminiya ta rika bayar da rahotannin kashe-kashe da garkuwa da mutane da ’yan bindiga ke yi a sassan Arewa da sauransu, inda ta’asa da makamai ta zama ruwan dare.

Buhari ya haye karagar mulki ne a 2015 da 2019 saboda dimbin kuri’un da Arewa ta ba shi.

Saukar Buhari ita ce mafi a’ala – Shugabannin Arewa

Kungiyar Dattawan Arewa (NEF) ce ta fara kiran Shugaba Buhari ya yi murabus, inda ta ce ya gaza tabukawa wajen kawo karshen ta’addanci da kashe-kashe a Arewa.

Wata sanarwa da Daraktan Labarai na Kungiyar, Dokta Hakeem Baba-Ahmed ya fitar ta ce kungiyar ta lura, “A kasashen da suka ci gaba, shugabannin da suka gaza samar da tsaro sukan ji abu mafi kyau da za su yi shi ne su sauka daga mukamansu.”

Bukatar Kungiyar NEF ta zo ne kwanaki kadan bayan da Kungiyar Kare Muradun Arewa (ACF), ta bukaci Shugaban Kasa ya ji tsoron Allah ya tsare rantsuwar da ya yi.

Kungiyar ACF ta shaida wa Shugaban Kasar cewa, “Muna jin babu bukatar mu yi kira ga Shugaban Kasa kan ya tashi da kare rantsuwar da ya yi.

“Ya san komai fiye da kowa kan illar rantsuwa da Alkur’ani kuma a ki tsare rantsuwar da aka yi ga Madaukaki.”

Saboda halin da ake ciki ne Mai Alfarma Sarkin Musulmi kuma Shugaban Majalisar Koli ta Harkokin Musulunci ta Najeriya Sa’ad Abubakar, ya ce Arewa ce mafi munin wurin zama, lura da yaduwar rashin tsaro.

Shi ma tsohon Gwamnan Jihar Jigawa, Alhaji Sule Lamido, ya nemi Shugaba Buhari ne ya nemi gafarar Allah idan yana so kasar nan ta zauna lafiya.

Lamido ya shaida wa gidan rediyon BBC London, cewa tilas ne Buhari ya ajiye girman kansa ya nemi gafarar Allah, inda ya ce mai yiwuwa ya yi wasu zunubai ne da suke shafar kasar nan.

Fitattun malaman Musulunci da suka hada da Shugaban Kungiyar Jama’atu Izalatil Bidi’ah Wa Ikamatis

Sunnah, Sheikh Abdullahi Bala Lau da Sakatare Janar na Jama’atu Nasril Islam, Dokta Khalid Abubakar Aliyu da Sheikh Abubakar Gero Argungu da sauran malamai sun bukaci Shugaban Kasar ya farka don ceto Arewa daga rugujewa.

Sai dai Ministan Labarai da Al’adu Alhaji Lai Mohammed, ya ce kiraye-kirayen ba wasu abubuwa ba ne face muguwar sanya siyasa a cikin harkar tsaro.

Ministan ya ce, “An zabi Shugaban Kasa ne a 2015 na shekara hudu kuma aka sake zabensa a 2019 na wasu shekara hudu. Babu wani matsin lamba da ke neman ya yi murabus da zai hana shi cikata

shekara hudunsa.”

 

Buhari ya sauka, ya nemi gafarar ’yan Najeriya – Dokta Bugaje

Jagoran Cibiyar Bincike da Bunkasa Ci gaba ta Arewa (ARDP), Dokta Usman Bugaje, ya ce ba ma sauka Buhari kawai zai yi daga Shugaban Kasa ba, sai ma ya hada da neman gafarar ’yan Najeriya kan lalata kasar nan.

Bugaje, wanda dan siyasa ne kuma jagoran kungiyar jama’a ya ce zai fi kyau ga kasar nan idan Shugaban Kasar ya yi murabus, yana mai cewa ya gaza kare tsarin mulkin kasar nan, wanda ya dora masa nauyin tsare rayuka da dukiyoyin ’yan Najeriya.

“Yana bukatar ya sauka saboda ya zo ya ruguza kasar nan. Me zai kuma sake yi? Akwai bukatar mutane su tambaya me zai tsaya yi.

“Ana yanka mutane amma ba za ka iya hawa jirgi ka je ka yi musu ta’aziyya ba, sai dai ka tura ’yan aike. Sojojinka sun gaza amma har yanzu kana zaune a can.

“Ya yi rantsuwar tsare tsarin mulkin da ya ce babban aikinka a gwamnati shi ne kare rayuka da dukiya. Ba ka yin haka amma kana kan kujerar; me kake yi?” Ya tambaya.

Tsige Buhari ya kamat a yi; ya yaudari jama’a – Kadzai

Da yake magana kan lamarin Shugaban Matasa na Ikilisiyyar ’Yan Uwa ta Najeriya (EYN), da ke Lafiya a Jihar Nasarawa, kuma Shugaban Matasa na Kungiyar Kiristocin Arewacin Najeriya (CNNC), Injiniya Daniel Kadzai, ya shaida wa Aminiya cewa Buhari ya yi mummunar gazawa.

Ya ce, ya kamata a hanzarta tsige Shugaban ba tare da bata lokaci ba, saboda muguwar gazawa.

“Hasali ma masu kiran ya sauka sun cire tsammani ne daga Majalisar Dokoki ta Kasa, in ba haka ba, yaya za su bar Buhari ya ci gaba da mulki bayan aikata dimbin abubuwan da suka cancanci a tsige shi?

“A shekarar 2016, Buhari ya kebe Dala biliyan 2 don yaki da ta’adanci ba tare da amincewar majalisa ba.

“Kuma tsarin mulki ya amince ma’aikaci ya ajiye aiki bayan shekara 35 ko ya cika shekara 60 a duniya, amma yau manyan hafsoshin tsaro sun tsallake haka a daidai lokacin da ake fama da abin kunya kan gazawa.

“Sun gaza sosai wajen gudanar da aikinsu duk da dimbin kudin da aka kebe musu.

“A karkashinsu wani dan uwansu Janar ya yi kukan rashin makamai a fagen daga kuma aka yi masa shari’a ta soja aka hukunta shi.

“Sojoji da yawa da suke yakar ’yan ta’adda sun kashe kawunansu saboda takaici,” inji Kadzai.

Ya ce, kiran manuniya ce cewa Buhari ya yaudari ’yan Najeriya musamman dattawan Arewa da

kuma galibin shugabannin addini da suke surutai a kafafen sadarwar zamani don ya kai ga gadon mulki.

“Ka san Sarkin Musulmi bai cika magana ba, sai in wani abu na faruwa. Hatta Sarkin Katsina ya kusan raba-gari da Shugaban Kasar. Tabbas wani abu na tafiya ba daidai ba,” inji shi.

Gazawar Buhari ta yi munin gaske – Masana

Shi kuwa Farfesan Kimiyyar Siyasa kuma Shugaban Sashin Harkokin Dalibai Dokta Abubakar Umar Kari, ya ce kiraye-kirayen Buhari ya sauka alama ce ta karuwar ’yan Najeriyar da ba su gamsu da Shugaban Kasar da gwamnatinsa ba.

“Mutane ciki har da wadanda a baya ’yan-a-mutum Buhari ne suna kokawa sosai, an kunyata su sun fusata kan yadda yake rikon sakainar kashi ga tabarbarewar tsaro a kasar nan.

“Kuma gwamnatin ba ta nuna da gaske take ko za ta iya magance matsalar, wannan hali da ake ciki bay a yi wa mutane dadi,” Kari ya shaida wa Aminiya.

Ya ce duk da cewa ’yan adawa ke yada kiraye-kirayen tare da wadanda suke da wata kullalliya da Shugaban Kasar, kiraye-kirayen na kara samun goyon baya ta yadda hatta magoya bayan Buharin sun shiga sahu.

Ya ce, “A kaikace ’yan bindiga da ’yan ta’adda sun mamaye kasar nan, inda suke kisa da ta’asa da kuma ta’addanci a kan jama’a, yayin da gwamnati ke nuna halin ko-in-kula ko ta gaza ko kuma a takaice ta magance kalubalen.”

’Yan-a-mutun Buhari su juya masa baya

Ya ce kiraye-kirayen sun yi matukar jawo koma-baya ga Shugaban musamman lura da cewa hatta mutanen Arewa sun shiga sahun masu yi.

“Dimbin ’yan-a-mutun Buhari yanzu suna kiran ya sauka. Wannan ya nuna muni da zurfin rashin

gamsuwa. Kuma hakan na nuna irin gazawar Shugaban.

“Matukar ba a yi wata hobbasa cikin gaggawa ba, tarihi ba zai yafe wa Shugaban Kasar da ke samun dimbin goyon baya da fahimta daga jama’a ba.

“Wajibi ne Buhari ya hanzarta daukar mataki mai zafi. A hanzarta dawo da zaman lafiya. A fuskanci miyagu a murkushe su. In ba haka aka yi ba ’yan Najeriya ba za su gamsu ba,” inji shi.

Kamar Kari, Dokta Tukur Abdulkadir wani masanin kimiyyar siyasa a Jami’ar Jihar Kaduna (KASU), ya ce masu kiraye-kirayen Shugaban Kasar ya sauka suna yi ne saboda fusata, wadda ya ce manuniya ce kan kuncin da ke shafar ’yan Najeriya.

Ya ce kiran a fili na nuna cewa Shugaba “ya yi muguwar gazawa,” wajen biyan bukatu da fatar da jama’a ke da ita game da shi.

Buhari ya gaggauta sake tunani’

“Ina jin babu bukatar ya yi murabus a wannan hali, amma gaskiya wannan babbar manuniya ce da ke bukatar ya sake tunani,” inji shi.

A Majalisar Dokoki ta Kasa wadda Jam’iyyar APC ke da rinjaye za ka ga matukar damuwa da rashin jin dadi sosai, hatta a cikin ’ya’yan jam’iyyarsa.

“Idan ba a yi takatsantsan ba, ’yan Najeriya za su koya wa APC irin darasin da suka koya wa PDP a hekarar 2015, matukar ba su farka ba,” inji shi.

Masanin kimiyyar siyasar ya shawarci Shugaban Kasar ya sake tunani kan yadda yake gudanar da harkokin mulki kuma ya daina mayar da harkar mulki wani abin kashin kai.

“Idan a matsayinsa na mutum ya gamsu da sadaukarwar manyan hafsoshin tsaro, abin da ke faruwa a can kasa a karkara yana nuna sabanin haka ne.

“Mutanen Najeriya shi suka zaba, ba su zabi Janar Buratai ko Iya Mashal Saddique ko sauran manyan hafsoshin tsaro ba.

“Don haka ya jingine bukatarsa ta kashin kai ya biya bukatun mafiya yawan jama’ar kasa, in ba haka ba, za a ci gaba da caccakar gwamnatinsa.

“Ina da tabbacin ba zai so a kalle shi nan da shekara uku masu zuwa a matsayin daya daga cikin mafiya

munin shugabannin da kasar nan ta taba samu ba, ko wanda sakacinsa wajen harkokin mulki ya jefa mu a halin da muke ciki a yau ba,” inji shi.

Ya kamata a kori kashi 80 na ministocin Buhari – Bashir Tofa

Dattijo Bashir Othman Tofa, ya shawarci Shugaba Buhari ya gaggauta maye gurbin akalla kashi 80 na majalisar ministocinsa da shugabannin ma’aikatun gwamnati domin kawo karshen dimbin matsalolin da suka zama karfenkafa ga gwamnatinsa.

Bashri Tofa, wanda ya yi takarar Shugaban Kasa a Jam’iyyar NRC lokacin zaben 12 ga Yunin 1993 da gwamnatin soja a karkashin Janar Ibrahim Babangida ta shirya kuma ta soke, ya ce ba wai kawai za a sallami ministocin da shugabannin ma’aikatun haka nan kawai ba ne, “lallai ne a yi musu binciken kwakwaf.”

Da yake martanin kan kiran da ake yawan yi na Shugaba Buhari ya yi murabus, dattijon cikin hirarsa da Aminiya a Kano, ya ce ba daidai ba ne a bukaci Shugaban ya yi murabus a daidai tsakiyar wa’adinsa saboda Najeriya na tafiya cikin tsarin dimokuradiyya ne.

“Mun zabe shi, kuma a 2023 za mu zabi wani mutum na daban. Ba ma zabar Shugaban Kasa kuma a daidai tsakiyar wa’adinsa mu bukaci ya sauka. Jira za mu yi domin yin waje-rod da su a zabe na gaba.

“Idan Shugaba Buhari ya sauka a yanzu, wane ne zai zama Shugaban Kasa? Mataimakin Shugaban Kasa wanda shi ma jigo ne a gwamnatin, ko kuma wane ne?” ya tambaya.

Ya ce: “Tunda Shugaba Buhari yana da akalla shekara biyu ko fiye kafin kare wa’adinsa na biyu, kawai abin da ya kamata mu yi shi ne mu lalubo hanyar ankarar da shi wajen daukar matakai kan al’amuran da suka fi damunmu, kamar rashin tsaro da durkushewar al’amuran gwamnati da kuma yaki da cin hanci na ’yan mowa da ’yan bora.

“A gare ni, zai yi abin da ya dace wajen sauya majalisar ministocinsa kafin shekarar nan ta kare sa’annan ya maye gurbin dukkan ministocinsa na wa’adinsa na farko da sababbin jini masu hazaka da nagarta.

“Dole ne ya kauce wa nada gogaggun ’yan siyasa da kuma abokan arziki. Kwarewa da sanin makamar aiki da kuma kishin kasa ya kamata su zama ma’aunin nada su.

“Akalla kashi 80 cikin ministoci da shugabannin ma’aikatun gwamnatinsa ya kamata a sallama, kuma lallai ne a yi musu binciken kwakwaf.

“Kowane sabon minister da shugaban wata ma’aikatar gwamnati a shaida masa baro-baro abin da ake son ya cimmawa kafin karewar shekarar 2021, da kudin da ake da su a kasa.”

Dattijon ya ce yawaitar kiraye-kirayen Shugaban ya sauka “saboda abin da ake ganin ya bayyana na nuna nuna halin ko-oho kan wahalhalun ’yan Najeriya da rashin tsaro da karuwar zarmiya da kuma take doka da yin amfani da iko ta hanyar da ba ta dace ba, musamman jiga-jigan gwamnati, kamar kamewa da tsare mutane kawai domin sun bayyana ra’ayinsu kan wadansu da ke kan madafun iko, kamar lamarin Mahdi Shehu.

“Amfani da doka da kuma tankwasa ta ta hanyar da ba ta dace ba na daya daga cikin ummul haba’isin koma baya.

“Ina mamakin yadda suka manta cewa mulki karba-karba ne.

Akwai matsala a tattare da Buhari, inji Bashir Tofa

“Ina yi masa addu’a sosai da kuma na lafiyarsa. Ina ganin akwai matsala tare da shi. Ba mai yiwuwa ba ne a ce da gangan yake nuna halin nasa. Akwai miyagun mutane da dama da suka kewaye shi.

“Ina kuma kira ga kowa ya yi masa addu’a. Shawarata gare shi ita ce ya natsu ya tafiyar da al’amuransa. Kasar nan tana fadawa rami, kuma shi ne zai zama abin zargi kuma wanda za a tsinewa,” inji Tofa.