Wasu daga cikin ’yan Najeriya da suka samu horo a kan fannin likitoci a kasashen waje sun bayyana yadda aka sanya rashin gaskiya a jarabawar da suka rubuta samun lasisin gudanar da aikin likitoci a kasar bayan horo na mako 16 da suka yi.
’Yan Najeriyar da suka samu horo a makarantun kasashen waje wadanda suka kai kimanin 200 wadanda suke cikin wadanda suka fadi jarabawar sun ce cibiyar likitoci ta kasa tun farko ta shirya za ta kayar da mafi yawancinsu.