Wani matashi da ke Sana’ar dinki a unguwar Fagge da ke jihar Kano, Salisu Hussaini, ya rasa hannunsa na dama sakamakon rabon wani fadan da ya kaure tsakanin mutane biyu, inda har daya yayi ya sha alwashin kashe dayan.
Lamarin dai ya farune a ranar 30 ga watan Maris, inda matasan biyu – Abubakar Ayuba, wanda akafi sani da Namama, da kuma Abdullahi Muhammad, wanda ake wa inkiya da Alhaji Ozil – suka yi fadan, inda shi Namaman ya ce sai ya kashe abokin fadan nasa.
- “Za mu kashe fasinjojin jirgin kasa idan gwamnati ta ki biya mana bukatu”
- NAJERIYA A YAU: Ko watsi da tsarin karba-karba zai kai PDP tudun mun tsira?
Sai dai matashin mai kimanin shekara 21, ya gamu da wannan iftila’in ne yayinda yake wa Namama nasiha a kan yunkurin cewa zai yi kisan kai, inda a nan take ya soka masa wuka a hammata wanda yajawo masa mummunan rauni.
Da yake bayyanawa Aminiya yadda lamarin ya faru, Salisu, wanda yake kwance a asibiti ya fashe da kuka, inda ya bukaci hukuma da ta bi masa hakkinsa, domin kuwa bai san yadda rayuwa za ta yiwu a yayinda ya rasa hannun nasa ba.
“A lokacin da na ga suna fadan, sai na yi kokarin fada wa shi Namama gaskiya a kan bai kamata ya rika ikirarin kashe dan Adam ba, kuma na rokeshi da ya daina.
“Nan take kawai sai na ji ya zaro wuka ya soke ni a kafadata. Dafarko ma so ya yi yas ameni a ciki, sai na ture shi da kafata.
“Daga nan kuma sai aka kai ni asibiti inda suka ce sai ’yan sanda sun zo za a yi min magani. Bayan kwana biyu da yin dinki a wajen sai ciwon ya dauki wani sabon yanayi.
“Kamar dai jijiyar wajen ta tsinke, daga nan ne muka je asibitin Murtala, inda su ma suka ce sai dai muje asibitin Koyarwa na Malam Aminu Kano, inda daga nan ne aka dawo da mu nan asibitin kashi, kuma suka tabbatar da cewar sai an yanke hannun.
“Bayan sun tabbatar sai an yanke hannun, sai suka ce na kira mahaifiyata mu sa hannu. A lokacin ba na cikin hayyacina, to a hakan dai nasa hannu ita ma mahaifiyata ta sa.
“Yanzu kalli yadda na zama, daga rabon fada na zama mai hannu daya,” Salisu ya fada yana kuka.
Ita ma mahifiyarshi, Zulaihatu Abubakar, ta ce yanayin da dan nata ya shiga abu ne na tsahin hankali, inda ta ce su na kira ga gwamnati da ta bi musu hakkinsu.
“Ya yi yunkurin kashe shi, kawai dai Allah ne ya kiyaye. Dana tela ne kuma da wannan sana’ar ya dogara. Yanzu ta yaya zai rayu a haka? Ba za mu taba yafe masa ba, kuma ya cutar da mu. Muna bukatar a bi mana hakkinmu.”
Rundanar ’Yan sandan Jihar Kano ta tabbatar da faruwar al’amarin, inda ta ce tuni ta kama wanda ake zargi da aikita laifin.
Kakakin rundunar, SP Abdullahi Haruna Kiyawa ya bayyana wa Aminiya cewar Kwamishinan ’Yan Sandan Jihar, Sama’ila Shu’aibu Dikko, ya ba da umarni inda aka mayar da wanda ya aikata laifin zuwa Shashen Binciken Manyan Laifuka na rundunar, inda kuma ake gudanar da bincike.