Wani matashin tela da ya fara sana’ar bayar da kayan sawa na haya a Kano ya ce ya ce harkar tasa na kara samun tagomashi.
Ibrahim Bature Yakubu ya ce akalla mutum 300 sun tuntube shi a cikin mako guda da bude wurin da ya fara a ranar 24 ga watan Agusta, 2020.
“Na lura cewa akwai kashe kudui mutum ya sayi yadi ya dinka, shi ya sa ni nake saye nake dinkawa sannan in bayar da hayar kayan.
“Muna bayar da hayar atamfar mata ko shadda ta maza a kan N1,500, Getzner kuma N3,000 sannan lokacin haya daga 9.00 na safe ne zuwa 10.00 na dare”, inji Ibrahim.
Jaridar intanet ta Kano Focus ta ruwaito cewa Ibrahim mazaunin unguwar Taludu Layin Alhaji Bature a garin Kano, ya samu kwarin gwiwar fara sana’ar ce da jarin N30,000 da nufin samun abun dogaro da kuma samar wa mutanen kayan fita kunya a wuraren buki da kuma halartar sauran taruka.
Matashin ya ce da farko mahaifansa sun dauke shi mashiririci da ya shaida musu abin da yake son yi, amma hakan bai sa ya karaya ba cewa abin da zai yi zai biya wa mutane bukata.
Ya yi kira ga matasa da su dage da neman na kansu ta hanyar kasuwanci, domin “jiran sai mahaifanka sun ba ka ba zai wadatar da kai ba”, inji shi.