✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda nake kuka a fim- Nafisa Abdullahi

A ranar Asabar ne kafar sadarwa da ke twitter mai suna ‘Kannywoodscene’ ta gayyato fitacciyar jarumar fina-finan Hausa Nafisa Abdullahi, inda masu kallo suka rika…

A ranar Asabar ne kafar sadarwa da ke twitter mai suna ‘Kannywoodscene’ ta gayyato fitacciyar jarumar fina-finan Hausa Nafisa Abdullahi, inda masu kallo suka rika yi mata tambayoyin da suka shafi harkar fim da kuma rayuwarta.
Jarumar ta ba da amsa cikin kwarewa da wani salo mai kayatarwa. An gudanar tambayoyin ne cikin yaren Ingilishi.
Abin da ya fi burge jama’a shi ne, kai tsaye ta rika amsa tambayoyin da aka yi mata ba tare da inda-inda ba, inda a wadansu lokuta takan hada da barkwanci.
Ko me ya sa take kuka a fim koyaushe, shin hakan ba ya ba ta wahala? Sai ta ce: “Kuka a fim ba ya ba ni wahala, saboda wata baiwa da nake da ita ce, nakan yi shi a duk lokacin da na ga dama. Wani lokaci nakan rika raya abin da yake cikin labarin kamar da ni yake faruwa da gaske, hakan ma ya dada taimakawa wajen iya kukan da nake yi a fim. Na karanta yadda ake aktin din fim a jami’a, don haka ina da dabarun yadda ake yin aktin. Idan kana fim ya zama dole ka yi abin da zai sanya jama’a su dauka da gaske ne, hakan zai sanya fim din ya fi tasiri a rayuwarsu. Rabona da kuka kwana hudu ke nan, kodayake a fim na yi ba a zahiri ba.”
Ta ce ranar da ba ta yin komai takan zauna a daki ta rika kallon fina-finai, ko ta ziyarci ’yan uwa da abokan arziki, sannan tana da yakinin wanda ba dan fim ba zai iya rike fitacciyar jaruma a bangaren aure.
Jarumar ta ce bayan lakabin Nafisa Sai Wata Rana ana kuma kiran ta da lakabin ‘Feener mai gashin Turawa’ da ‘yar baka da kuma Ice kueen.
Ta ce harkar fim ta nuna mata cewa akwai mutanen bogi masu yawa a duniya da suke neman jama’a da sharri, ta ce abin da yake kara mata karfin gwiwa shi ne yanayin yadda masoyanta suke karfafa mata gwiwa, suke kuma karuwa.
Ta ce abin da ta tsana shi ne a mayar da ita sakarya wadda ba ta san ciwon kanta ba.
Tambayoyin da jarumar ba ta amsa ba su ne: wacce masana’anta ta fi so tsakanin ta Indiya (Bollywood) da kuma ta Amurka (Hollywood) da wane irin miji take so da kuma sunan motar da take hawa yanzu.